Gyaran fata (2)

Daga AISHA ASAS

A satin da ya gabata mun share fage kan sha’anin da ya jiɓinci lafiyar fatarmu da yadda ya kamata mu kula wurin ganin ba mu sanya ta yanayin da ka iya cutar da ita ba. Mun kuma kawo wasu daga cikin ‘yan dabarun gyaran fata wanda mu ke fatan kammala wannan darasin da ƙarin wasu daga ciki.

Uwar gida za ta iya amfani da kankana wurin magance baƙin fata irin wuraren gwiwa, hannu, ƙafa da sauran su, idan ta haxa ta da lemun tsami (akwai fatar da ba ta son lemon tsami, idan ta ki na ciki za ki sanya kaɗan ne, wanda zai sa ba zai ji wa fatar ciwo ba), tsayin mintina 15 sai a samu tawul mai tsafta a goge da ruwan ɗumi. A jira wasu mintuna goma kafin ayi wanka.

Uwar gida ki samu ditol (dettol), sabulun gana, farar albasa, garin zogale. Ki haɗa su wuri ɗaya, amma ditol ɗin a sanya kaɗan sosai, za ki ga ya haɗe tamkar sabulu, ya yi ƙarfi. Ki dinga wanke fuska da shi, ko wanka bakiɗaya. Zai sanya fata kyau da ƙyalli.

Shin uwar gida na da masaniyar cin tumatur a kowacce rana na sanya fata ƙyali, musamman idan kina cin lafiyayun tumaturin wanda bai fara lalacewa ba.

Kazalika, za ki iya amfani da tumatur don sanya fuskarki kyawon kwalliya. Za ki markaɗe tumatur mai kyau, sai ki sanya zuma ki kaɗe su sosai, ki samu laka mai danƙo ki haɗa su, za ki ga ya yi kauri idan kin sa lakar da za ta ishe haɗin. Ki shafa a fuska da wuya, sai ki ba shi mintuna goma, za ki ga ya bushe matuƙar ya samu iska.

Sai a cire shi a hankali, zai taso da datti da gashin fuska, don haka a kaucewa sawa a ido ko gira, zai taimaka idan kin ɗora yankan kokumba a ko wane idon ki a lokacin da kika gama, kuma wannan haɗin zai fi kyau idan wani ya shafa ma ki. Daga nan sai ayi wanka bayan mintuna biyar.

Ki nemi ayaba mai kyau ki markaɗe shi, ki sa madarar shanu, ki fasa kwai ki yi amfani da farin ba gwaiduwar ba, ki sanya ruwan lemon tsami kaɗan, a haɗe su wuri guda, sai a shafe jiki gabaɗaya da shi, tsayin awa ɗaya da rabi kafin ayi wanka da ruwan ɗumi.