’Yan barandan siyasa sun kai hari taron PDP a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Litinin ne wasu gungun ’yan daba da ake kyautata zaton ’yan barandan siyasa ne suka tada hankali a filin wasa na Ranches Bees, harabar da jam’iyyar PDP ta gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen ɗan takararta na Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.

Mahalarta taron dai sun riƙa neman mafaka yayin da ’yan daban ɗauke da adduna da sauran makamai iri-iri suka riƙa jifan mutane da duwatsu.

Haka kuma, an ruwaito cewa, ’yan daban sun yi wa jama’a da dama ƙwacen wayoyinsu na hannu yayin taron.

Tuni dai tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Atiku ya yi martani kan wannan lamari da ya bayyana a matsayin abun takaici daga masu adawa da jam’iyyar PDP.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Atiku ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya gargaɗin magoya bayan sauran jam’iyyu da su shiga taitayinsu.

Atiku wanda ya tunatar da yadda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da tabbatar da aminci yayin yaƙin neman zaɓe, ya ce aukuwar wannan lamari a yanzu ya saɓa wa tsari na dimokuraɗiyya.

Mai Magana da Yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce, tuni sun tura jami’ansu harabar domin kwantar da tarzomar.