Ba mu da kuɗin motar koma wa jami’o’inmu, inji Malaman jami’a

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ta nuna damuwarta kan rashin biyan mambobinta albashinsu na tsawon wata takwas, wanda a cewarta hakan ya sa malaman rasa kuɗin motar da za su koma bakin aiki bayan janye yajin aikin da suka yi.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugaban ASUU na Ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, a lokacin da yake jawabi dangane da batun janye yakin aikin da suka yi a tashar Talabijin ɗin Channels ranar Lahadi.

Idan dai za a iya tunawa, Manhaja ta rawaito batun janye yajin aikin da ASUU ta yi a Juma’ar da ta gabata bayan shafe watanni takwas tana neman cimma buƙatun mambobinta a wajen Gwamnatin Tarayya.

Yayin yajin aikin, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu Adamu, ya yi iƙirarin gwamnati ta cimma galibin buƙatun ASUU da suka haɗa da sakar wa ASUU kuɗi biliyan N50 don biyan alawun ɗin malamai da sauransu.

Sai dai duk da haka ASUU ta ki yarda ta janye yajin aikin a wancan lokaci saboda rashin biyan albashin malaman na adadin watannin da suka yi suna yajin aikin.