Dandalin shawara

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Mummyna Aysha Asas sannu da aiki. Ya kike. Fatan kina cikin jin daɗi. Na kira layinki ya fi a qirga don sanar da ke tawa damuwa sai dai ba a ɗauka ba. Ni dai shekarata 17, kuma dan Allah kar ki yi mun mummunar fahimta. Wallahi tun last year mahaifiyar best friend ɗita ta neme ni don mu yi les, kuma ta ja ra’ayina har sai da na amince da ita.

Tun daga nan ta ke zuwa tana ɗauka ta duk lokacin da babu karatu, ko mu je hotel ko ta kai ni wani gida. To matsalata dai Ina jin tsoron friend ta san abinda mu ke yi. Don yanzu har gidanta ta ke zuwa da ni. Ina neman shawarar yadda zan daina don Allah Ina son friend ɗita, na san rasa abotamu duk ranar da ta san abinda na ke yi da mahaifiyarta. Don Allah mummyna ki ba ni shawara.

AMSA:

Da farko dai ba zan faɗi abin da kike son ji ba, wato laifin dukka na mahaifiyar lawarki ne ba, kasancewar ki mai ƙarancin shekaru, ta yi amfani da yarinyar ki wurin sanya ki abin da ba ki da ra’ayi. Idan na gaya ma ki hakan na yi ma ki ƙarya, duk da cewa ta fiki laifi, hakan ba yana nufin ba ki da laifi ko kaɗan ba.

Abota na nufin amana, kuma ita amana ba a shekaru ta ke ba, ba ta da wani sharaɗi da sai ka kai shi ake tsamanin samun ta a tattare da kai ba. Idan har kin kasance mai sanin ya kamata, bai kamata da hankalinki ba ƙarfi aka yi amfani da shi wurin tursasa ki ba ko wani abin maye ba, ki iya amincewa da mahaifiyar abokiyarki ta amana a irn wannan mu’amala.

Abin da ya kamata ki fara tambayar kanki a lokacin da ta nuna ra’ayinta kanki, ya ƙawata zata ji idan na aikata hakan da mahaifiyarta? Wane irin hali zata tsince kanta?

A zuciyarki ki yi musanyar wuri da ita, ma’ana ki tambaye kanki idan ke ce mahaifiyarki ta nemi hakan da ƙawarki ya za ki ji? Amsar da kika ba wa kanki ce ya kamata ki yi amfani da ita wurin yanke hukunci matuƙar ba ki kasnce a cikin mutane masu son-kai ba.

A taƙaice abin da kika aikata tsabar son kai da rashin amana da kike da shi ne ya jagoranci wannan ɗanyen aiki da kika yi, don haka sai kin fara da amincewa da su tare da ɗaura aniyar canzawa ne, sannan duk wani abu zai iya yin tasiri.

Idan na koma ɓangaren iyaye, zan iya cewa kamar kullum mu na da kaso a mafi yawan ayyukan da ‘ya’yanmu ke aikatawa. Wannan ne karo na kusan na huɗu ko biyar da na samu irin wannan neman shawara duk da cewa suna da mabanbantan tushe da asali, amma dukkansu sun tafi kan matasan ‘ya’ya da suka faɗa mummunar hanya ta sanadiyyar sha’awa.

Sha’awa hallita ce kamar yadda tsari da zubin jikin ɗan Adam yake. Kowa da irin yadda aka hallita masa ta sa, akwai yaron da ya turo min da saqon neman shawara, mai shekaru 15, yana sanar da ni yana da ƙarfin sha’awa da har manyan mata birge shi suke, sai dai har zuwa lokacin iyayenshi na haɗa shi kwanciya da ‘yan’uwanshi mata ko baƙi mata idan suka zo.

Ba kuma don babu wadatar muhalli ba, wai saboda tursasa zuciyarshi amincewa da har lokacin shi yaro ne, kuma yana da doguwar tafiya kafin ya kai ga zancen aure. Abin takaici mahaifiyarshi ta yanke wannan hukuncin ne a lokacin da ta kama shi yana roƙon mai aikinsu ta bari ya taɓa ta zai bata dubu ɗaya.

Sannan mahaifiyar wani yaro ɗan shekara 19 ta neme ni kan sha’anin matsalar ɗanta da ita ta ɗora ta babin tavin hankali. Yaron idan ana biki ko wani taro na dangi, yakan zauna ne a ɗakin da ‘yan matasan mata ke zama na daga dangi da abokan arziki, amma fa mafi yawan su sun girmeshi.

Matuƙar babu iyaye a ɗakin, to zai dinga ciro al’aurashi a gaban su. Abin tun matan na haƙuri har suka fara faɗa da shi, har aka fara kawo ƙararshi ga mahaifiyar ta shi. A taƙice dai bayan dogon zama da tattaunawar da na yi da yaron na fahimci ba wata hauka face tsabagen sha’awa da ke cin shi.

Ƙarancin shekarunshi ya sa yake ganin ta wannan hanyar zai iya samun wadda zata kulashi. Abin da zai ba ku mamaki shine, yaron da kansa ya nemi mahaifiyarshi ta yi masa aure ko da a cikin gadon da ya gada daga mahaifinshi ne, ita kuwa ta tabbar ma shi sai ya kammla karatun jami’a kuma ya fara aiki ko kasuwanci.

A nan ba wai Ina son in nuna illar ƙin yi wa yaron da bai da sana’a aure ba. Tabbas wannan ce hanya mafi daidai, asalima abin kula da iyali na daga ɓangaren ciyarwa da tufatarwa na daga cikin sharuɗan aure, sai dai iyaye su sani ba akan kowanne yaro wannan sharaɗi yake hawa ba.
Za mu ci gaba