Wani rahoton aiki mai burgewa

Daga BELLO WANG

Rahoton da babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin (JKS) Xi Jinping ya gabatar a jiya Lahadi, a yayin buɗe babban taron wakilan JKS karo na 20 yana da burgewa sosai, saboda cike yake da bayanai masu nasaba da tunanin dora muhimmanci kan moriyar jama’a.

A cikin rahoton, yayin da ake bayyana nasarorin da jam’iyyar ta cimma a shekarun baya, an fi ɗora mihimmanci kan yadda ta kare rayuka da lafiyar al’umma daga cutar COVID-19, da kawar da talauci a ƙasar Sin, da kafa tsarin ilimi, da aikin lafiya, da ba da tabbaci ga ingancin zaman rayuwar jama’a mafi girma a duniya.

Kana a ɓangaren ayyukan da za a yi a nan gaba, an jaddada buƙatar daidaita matsalolin da suka fi damun jama’a, da samar da isassun damammakin raya kai.

Ban da bayanan rahoton, wasu wakilan JKS mahalartar taron, su ma sun shaida wa manema labaru, yadda tunanin dora muhimmanci kan moriyar jama’a yake yin amfani a ƙasar.

Zulyati Simayi, wakiliyar JKS ce da ta zo daga jihar Xinjiang ta ƙasar Sin.

Ta yi bayani kan labarin wata yarinya ‘yar Uygur: Wannan yarinya da aka haifa a gundumar Wensu ta garin Aksu, bayan da ta kammala karatun sakandare, ta shiga makarantar koyar da ilimin sana’a, inda ta koyi fasahar hannu ta ɗinki domin kawata tufafi.

Daga baya ta fara aiki a ma’aikatar samar da tufafi don neman inganta fasaharta ta ɗinki.

Zuwa yanzu, bisa tallafin gwamnati, ta kafa wata ma’aikatar ɗinkin tufafi ta kanta, inda ta samar da dimbin guraben aikin yi ga matasa.

A nata ɓangare, Jiang Lijuan, matar dake riƙe da mukamin dagacin ƙauyen Xiajiang dake lardin Zhejiang na ƙasar Sin, ta yi bayani kan yadda mutanen ƙauyenta suke ta cimma burin samun ƙarin kuɗin shiga.

Ta ce a shekarar 2021, kuɗin shigar duk mutum ɗaya a tsawon shekara a ƙauyenta ya kai dalar Amurka 6,522, jimillar da ta ninka ta shekarar 2003 har sau 14.

Wannan lamari ya nuna yadda jam’iyyar mai riƙe da ragamar mulki a ƙasar Sin, wato JKS, take ƙoƙarin sanya ci gaban tattalin arzikin ƙasar a matsayin abun da zai amfani kowanne mutum na ƙasar.

Ko shakka babu, yadda ake mai da hankali kan moriyar jama’a, ya sa ƙasar ta Sin ta dora muhimmanci kan makomar bai ɗaya ta ɗaukacin bil Adama, ta fuskar manufar hulɗar ƙasa da ƙasa ta ƙasar.

Wannan tunani shi ma yana cikin rahoton JKS dake kan karagar mulki a ƙasar.

A cewar Lin Zhanxi, wakilin JKS, kuma ƙwararre a fannin nazarin fasahohin aikin gona, shi da tawagarsa na ƙoƙarin yayata fasahar noman laimar kwaɗo a duniya, bisa goyon bayan da gwamnatin ƙasar Sin ta ba su.

Dalilin da ya sa ake yin haka, shi ne wannan fasaha ta taka muhimmiyar rawa, a ƙoƙarin ƙasar Sin na fid da manoma daga ƙangin talauci.

Yanzu haka an horar da ma’aikata fiye da 12,000 a ƙasashe masu tasowa da dama, waɗanda suka yada fasahar zuwa wasu ƙasashe da yankuna 106.

Ta waɗannan misalai, ana iya ganin yadda JKS take ƙoƙarin kare moriyar jama’ar ƙasar Sin, gami da ta dukkan dan Adam, bisa babbar manufarta ta kokarin bautawa jama’a.

Wannan manufar ita ce dalilin da ya sa ta samu damar rike ragamar mulki a ƙasar Sin har tsawon shekaru 73, kuma take ci gaba da samun goyon baya daga al’ummar ƙasar Sin.