Haƙƙin tabbatar da zaman lafiya ya rataya a kanmu ne duka – Tinubu ga gwamnoni

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi gaba daya ke da alhakin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar.

Da yake jawabi yayin wata ganawa da Kungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) a gidansa da ke Legas ranar Talata, shugaban ya sake yin Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a jihar Filato.

Da yake jawabi ga gwamnonin, shugaban ya bayar da wani kakkausan umarni ga jami’an tsaro da su dakatar da kashe-kashen da ake yi a jihar Filato tare da kara zage damtse wajen zaqulo wadanda suka haddasa munanan abubuwan da suka faru a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi.

“Nijeriya na bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali domin ci gaba, Nijeriya ta mu ce kuma dole ne mu kula da ita.”

Bayan haka sai Tinubu ya jinjina wa Gwamnan Ribas Simi Fubara, kan yadda ya amince da a zauna lafiya a jihar.

By Editor