Gobara ta ƙone sakatariyar Ƙaramar Hukumar Ɗandume

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gobara ta kone mafi yawan ofishoshin sakatariya na Karamar Hukumar Dandume a jihar Katsina.   

Gobarar da ta tashi da yammacin ranar Lahadi da ta wuce ta kone ofishoshi 31na sakatariyar.                

Wasu a cikin ofishoshin da suka kone sun hada da na Shugaban Karamar Hukumar da na ofishin jagoran kansiloli da kuma dakin taro na karamar hukumar.                  

Sauran sun hada ofishin baitul mali da na wasu kansiloli.                          

Haka kuma akwai ofishin Daraktan ma’aikata da na mai biciken kudi duk na karamar hukumar sun kone kurmus.

Da yake duba ofishoshin da gubarar ta lashe shugaban karamar hukumar Basiru Musa tare da rakiyar wasu jami’an karamar hukuma ya nuna alhininsa game da iftala’in tare da kafa kwamitin mutum bakwai nan take domin su binciki musabbabin gobarar.             

Haka kuma kwamitin ya gano inda hannun wasu a ciki.                              

Shugaban karamar hukumar ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu da hannu a gobarar ko waye shi zai fuskanci hukuma.                   

Ba a dai rasa rai ko daya ba sai dai muhimman takardu na karamar hukumar sun kone.