Emefiele ya nesanta kansa daga zarge-zargen talauta Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya karyata zargin da Mai Binciken CBN Na Musamman da Shugaba Bola Tinubu ya nada ya yi masa, wato Jim Obazee.

Kwanan nan Obazee ya gabatar wa Tinubu rahoton harqallar da ya bankado Emefiele ya aikata a CBN, wadda aka yi zargin ya bindige biliyoyin nairori da biliyoyin daloli.

Cikin harkallar da Obazee ya bankado har da badakalar sauya launin kudi, wadda Obazee ya ce damfara ce kawai sata Emefiele ya kantara.

Da ya ke karyata zarge-zargen da Obazee ya yi masa Emefiele a ranar Lahadi ya yi ikirarin cewa labarinsa da aka buga “qage ne, karya ce, kuma karkatar da hankulan jama’a ne, don kawai a bata masa suna.”

Daya daga cikin lauyoyinsa mai suna Maxwell Okopara, ya shaida wa Daily Trust cewa Emefiele din ne ya fitar da sanarwar da kansa.

“Na karanta labarin, kuma dukkan abin da aka buga dangane da zarge-zargen da ake yi min, karya ce, kage ne kawai don a bata min suna, kuma soki-burutsun mai bincike ne kawai.”

Emefiele ya ce dukkan tsarin sauya launin kudi an yi shi kan ka’ida kuma bisa cikakken amincewa da goyon bayan tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari.

Ya ce dukkan makudan kudaden da ake zargin ya sata, sharri ake yi masa, kuma zai garzaya kotu domin ya nemi hakkinsa.

Baya ga zargin zamba da damfara a harkar sauya launin kudi, ana zargin Emefiele da nunke Naira tiriliyan 26.627 baibai. Sannan kuma an gano yadda ya boye biliyoyin daloli a bankuna 589 da ke Birtaniya da Chana da kuma wasu laifukan zamba da satar kudade.

A ci gaba da fallasa gagarimar satar da ake zargin Godwin Emefiele ya dirka a CBN, Mai Bincike na Musamman, Mista Obazee na zarginsa da yi wa Naira tiriliyan 26.627 kulli-kurciya, ta yadda ya nunke ‘yan Nijeriya da gwamnati baibai.

An kuma zarge shi da ajiye makudan kudaden Korona, wato COVID-19 a inda ba can ya kamata a boye su ba.

Kada dai a manta CBN ta bai gwamnatin tarayya bashin Naira tiriliyan 27 a zamanin gwamnatin Buhari, ba tare da sanin Majalisar Dattawa ba.

Manhaja ta buga labarin ‘Yadda Sabiu Tunde ya ba Emefiele shawarar a sauya wa Naira launi’.

A ci gaba da bankado harkallar gagarimar sata da gadangarkamar karkatar da makudan biliyoyin kudaden Nijeriya da ake zargin tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya tafka, Mai Binciken Harkalla na Musamman ya damka wa Shugaba Bola Tinubu rahoton abin da ya bankado a CBN.

Cikin rahoton, Mai Bincike Obazee ya bayyana cewa tun asali CBN ya aika wa Kwamitin Gwamnonin CBN shawarar za a sauya launin kudi.

Babban Daraktan Hada-hadar Kudade na lokacin, Ahmed Umar wanda ke karkashin Mista Folashodun ne aka sa ya rubuta masu wasikar a ranar 25 ga Agusta, 2022.

Kwatsam, wata daya bayan wasikar, sai Emefiele ya ce wai ya hadu da tsohon hadimin tsohon Shugaban Muhammadu Buhari, wato Sabiu Tunde a Fadar Shugaban Kasa, a ranar 6 ga Oktoba, 2023, wanda ya shaida masa cewa gara ma a sauya launin kudi.

“To a wannan ranar Gwamnan CBN din ya rubuta wa Shugaba Buhari shawarar sauya launin kudi, kuma a ranar ce ya sa wa takardar hannun amincewa.

“Sai dai kuma Buhari ya bada umarnin a buga kudaden a cikin gida Nijeriya. Sai dai kuma da aka tuntubi Kamfanin Buga Kudaden Nijeriya, wato Nigerian Security Printing and Minting Plc, ya ce aikin zai dauki lokaci kafin ma a tsara sabon launin tukunna.

“Jin haka sai Emefiele ya kinkimi aikin ya kai shi Birtaniya, ya biya fam fam na Ingila har 205,000 ladar zana fallen hoton launin Naira 200, Naira 500 da Naira 1,000.” Wannan fa ba a kai ga maganar bugawa ba ma tukunna.

Manhaja ta buga wani bangare na binciken, inda Mai Binciken Musamman ya ce ya gano kawai sauya launin Naira da Emefiele ya yi, zamba da harkalla ce kawai.

Mai Binciken CBN na Musamman, Obazee, ya bayyana a cikin rahoton binciken da ya gudanar cewa shirin sauya launin kudin da tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya bijiro da shi, harkalla ce kwai da zuma tantagaryar zamba.

Ya ce shirin ba a nemi amincewar Hukumar Gudanarwar CBN ba, kuma ba a nemi amincewa a rubuce daga shugaban lokacin ba, Muhammadu Buhari.

Ya ce hakan kuwa an kauce wa Sashe na 19 (1) na Dokar CBN, ta 2007.

“Kawai wata makarkashiya ce Emefiele ya shirya domin damfarar ‘yan Nijeriya, musamman manyan ‘yan siyasa. Kuma Emefiele ne ya shirya wannan zambar, shi da mataimakinsa a wancan lokacin, mai suna Folashodun Shonubi.

“Emefiele da Shinubi sun shirya zambar sauya launin kudi don su hana wasu manyan ‘yan siyasa kasa cimma burinsu. To amma sai abin ya zama masifa da bala’in kuncin rayuwa ga daukacin ‘yan Nijeriya.”

Obazee ya ce CBN ya yi sabbin kudaden na N200, N500 da N1,000, kuma Naira biliyan 61.5 ya kashe wajen buga kudaden, wadanda ya biya Naira biliyan 31.8 ga dan kwangilar. Kuma Naira biliyan 769,562 kadai na sabbin kudaden aka buga.

“Emefiele ya kwashi Naira 1,727,500,000 wai ya biya kudin lauyoyin biyo bayan shigar da CBN kara da aka yi ta yi, bayan ya sauya launin kudi,” haka Obasee ya bayyana a cikin rahotonsa.