Daga BASHIR ISAH
Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yaba wa Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiya Abdullahi Sule, bisa tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar, tare da jaddada cewa cigaban al’umma ba ya samuwa sai da zaman lafiya.
Shittima ya yi wannan yabo ne a yayin da yake kaddamar da hanya mai tsawon kilomita 5 da Gwamna Sule ya gina a yankin Masaka-Luvu, a Karamar Hukumar Karu da ke jihar a ranar Alhamis.
Mataimakin Shugaban Kasar ya ce abin a yaba ne ainun yadda Gwamna Sule ke ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a jiharsa duk da irin kalubalen da kasa ke fuskanta, musamman a wasu sassan arewacin kasa.
A nasa bangaren, Gwamna Sule ya nuna gamsuwa da farin cikinsa da kammaluwar hanyar Masaka-Luvu wanda hakan zai saukake wa al’ummar yankin sha’anin zirga-zirga.
