Daga BASHIR ISAH
‘Yan bindiga sun yi barazanar sake kai sabon hari a kauyen Jihar Filato kwana hudu da kai hare-hare a wasu sassan jihar wanda ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mutum 195.
Mataimakin Sakatare na kasa na kungiyar Middle Belt Forum, Stanley Kavwam, shi ne ya bayyana haka a tattaunar da aka yi da shi a tashar Arise Television a ranar Alhamis.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun aike da wasikar sanarwa kan za su kai hari a kauyen Pushit da ke yankin Karamar Hukumar Mangu a jihar.
Da yake amsa tambaya kan batun, Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred, ya shaida wa majiyarmu cewa suna sane da barazanar.
“Muna da bayanan sirri, amma muna aiki a kan batun,” in ji Jami’in.
Haka nan, wani mazaunin yankin ya shaida wa majiyarmu a ranar Alhamis cewa, lallai mazauna kauyen na da masanaiya kan wasikar barazanar da ‘yan bindiga suka aika musu.
