Haƙƙoƙin Ahlul Baiti a kan al’ummar Musulmi

Daga MUHAMMED BALA GARBA

Iyalan gidan manzon allah (Sallalahu alaihi wasallam) suna da wadansu haƙƙoƙi guda Uku (3) waɗanda suka zama wajibi a kan kowane musulmi. Ga su kamar haka:

kauna da Girmamawa: Iyalan gidan manzo suna da wananan matsayi a cikin al’umma, dake wajabta a kaunacesu da girmama su fiye da kowa. abubuwan da muka ambata a baya ma sun isa hujja a kan wannan. Ba sai mun nemi kafa wata sabuwar hujja ba.

yi musu salati tare da mai gidansu: yi wa ahlul Baiti Salati tare da manzon allah (Sallalahu alaihi wasallam) na daga cikin haƙƙoƙinsu a kan musulmi mai bin tafarkin Sunnah. Don allah (SwT) ya ce: “Lalle, allah da mala’ikunsa suna Salati ga annabi. ya ku waɗanda sukayi imani ku yi Salati a gare shi, kuma ku yi Sallama domin amintarwa a gare shi.” kuma manzon allah (Sallalahu alaihi wasallam) da ya bayyana wa Sahabbai yadda wannan Salati zai kasance, ya gaya musu su shigar da iyalansa. mun kawo wannan hadisin a can baya,

Biyayya: Biyayya da koyi dasu, shi ma wajibi ne, a kan duk wanda ke koyi da manzon allah (Sallalahu alaihi wasallam).

Wacce ce Nana Faɗima?

Ita ce Faɗimatul Zahra’u ‘yar shugan halitta annabi muhammadu (Baban alkasim), ɗan abdullahi ɗan abdulmuddalib ɗan Hashim ɗan abdumanaf ɗan kusaiyi ɗan kilab ɗan murrah ɗan ka’ab ɗan Lu’a’iyi ɗan Galib ɗan Fihri ɗan malik ɗan Nadri ɗan kinanah ɗan khuzaimah ɗan mudrikah ɗan Iliyas ɗan mudar ɗan Nazar ɗan ma’add ɗan adnan.

Wannan ita ce dangartakarta wacce babu sabani akai, kamar yadda kuma ba a yi sabani ba wajen cewa “adnan” ɗaya ne daga cikin zurriyar annabi Isma’ilu. (wato kenan dangantakan annabi (Sallalahu alaihi wasallam) ta haɗu da ta annabi Isma’ilu ɗan annabi Ibrahimu).

Haihuwarta:

An haifi Nana Faɗimatul Zahra’u (Allah Ya ƙara mata yarda) ne a ranar Juma’a, ashirin ga watan jimada Sani, shekaru biyu bayan aiko annabi muhammadu (Sallalahu alaihi wasallam). Bayan haihuwar manzo allah (Sallalahu alaihi wasallam) ya amshi ‘yarsa da farin ciki da amincewa, ya kuma sa mata suna Faɗima.

An haifeta kuma ta tashi a gidan annabci, ta tarbiyyantu a inuwar wahayi, da kyawawan ɗabi’u daga uwar muminai Nana khadija (allah ya kara mata yarda). Nana Fadima ta kasance mai dauke da ruhin manzo Allah (Sallalahu alaihi wasallam) da ɗabi’unsa, don haka ta zama mai gado da kuma tsananin kama dashi. Ban ga wanda ya fi kama da manzon allah (Sallalahu alaihi wasallam) a rashin magana da kyauta fiye da Nana Faɗima ‘yar manzon allah ba, a tsayuwarta da zamanta.

Ta kasance idan ta shiga wajen Annabi (Sallalahu alaihi wasallam) ya kan miƙe ya tarbe ta, ya zaunar da ita a wurin zamansa. Haka nan idan annabi ya shiga gare ta, ta kan mike daga wajen zamanta ta tarbe shi, ta zaunar da shi a wajen zamanta. “allah ya so Fadima ta fara yarintarta a wani yanayi mafi tsananin wahala da ƙuntata wa daga matakan da’awar Musulunci, kuma wanda mahaifanta suka fi shan wahala da cutuwa a cikinsa.

Ga dai Ƙuraishawa nan na tilasta takunkumi tattalin arziki a kan manzon allah da danginsa daga Banu Hashim da mayar da su saniyar- ware.

a wannan lokacin ne aka tsare Manzon Allah (Sallalahu alaihi wasallam) a Shi’abu abu Ɗalib tare da matarsa Nana khadija da ‘yarsa Nana Faɗima da sauran musulmi. Shekarun takunkumi sun wuce tare da matsanancin hali, har zuwa lokacin da manzo (Sallalahu alaihi wasallam) ya fita daga cikinsa tare da waɗanda ke tare da shi alhali allah ya rubuta masa nasara da galaba.

khadija kuwa ta fita daga cikin shi alhali shekarun sun yi mata nauyi, gajiyar takunkumi da matsalolinsa sun raunana ta. wannan ya sa ajalinta ya gabato. Allah ya zabar mata maƙwabtakarsa, inda ta rasu a wannan shekara, bayan ‘yan watanni kuma sai abu Ɗalib baffan annabi (Sallalahu alaihi wasallam), mai ba da kariya da taimakon musulunci, wanda manzo (Sallalahu alaihi wasallam) ya bayyana yadda ya yi rashinsa da faɗarsa cewa:

“Ƙuraishawa ba su fara matsamin ba har sai da abu Ɗalib ya yi wafati har sau biyu’’”(ya rasu).

Haƙiƙa Manzon Allah (Sallalahu alaihi wasallam) ya yi bakin ciki kuma ya ji kaɗaici saboda rabuwa da Nana khadija. Domin ya yi rashin khadija matarsa, masoyiyarsa kuma mai taimakonsa. kamar yadda ya yi rashin baffansa mai kariya gare shi, don haka ya kira wannan shekara da sunan shekarar bakin-ciki. Nana Faɗima, karamar ‘yar manzo allah (Sallalahu alaihi wasallam) (a wannan lokaci) haka ta rayu cikin wani ɓangare na wannan bakin ciki, ita ma ta yi makoki, don kuwa ita ma bala’in wannan shekarar ya taba ta, yayin da ta rasa uwa mai tausayi, alhali kafin nan ta koshi da kaunarta da lurarta, don haka (yanzu) ta lullubu da bakin-ciki da maraici. Sanannen abu ne cewa dole ne wannan rasuwa ta girgiza Nana Faɗima don kuwa ta rasa mahaifiyarta, ta rabu da cibiyar ƙaunarta, don haka sai dacin rabuwa ya cika zuciyarta ya kuma girgiza ta.

Babanta Manzon Allah (Sallalahu alaihi wasallam) ya dandana baƙin-cikin Nana Faɗima, yayin da ya ga ƙaramar ‘yarsa na zubar da hawayen rabuwa da mahaifiyarta, sai zuciyarsa mai tausayi ta yi kuna, jiyayyar nan tasa ta uba mai ƙauna ta gaskiya ta tabu, don haka sai ya kusanci Nana Faɗima don ya musanya mata abin da ta yi rashi na ƙauna da kusanci da kaunarsa da taushin zuciyarsa. Haƙiƙa Manzon Allah (Sallalahu alaihi wasallam) ya so Nana Faɗima kuma ita ma ta so shi, ya tausaya mata kuma ita ma ta tausaya masa.

Babu wanda ya fi Nana Faɗima kusa da shi kuma ba wanda yake so kamar ta. ya sha jaddada wannan alaka a cikin hadisansa yana bayyana matsayinta a cikin al’ummarsa. Ga kadan daga cikin abubuwan da ya fadi dangane da ita:

“Faɗima wani yanki ne daga gare ni, wanda ya fusata ta ya fusata ni.” Duba Bukhari hadisi na (3714).

Da kuma cewa: “Lallai Faɗima wani yanki ne daga gare ni, (duk) abin da ke cutar da ita yana cutar da ni “. Bukhari hadisi na (3714).

a wani wajen kuma cewa ya yi: “ya Faɗima, ashe ba za ki yarda da kasancewa shugabar matan duniya ba, kuma shugabar wannan al’umma da shugabar matan muminai. Bukhari hadisi na (3715 dana 3716).

“Faɗima na girma kaunar babanta na girma tare da ita, tausayinsa na ƙaruwa, kuma ita ma tana musanya masa wannan ƙauna, tana cika zuciyarsa da lura, don haka ya kira ta da Ummu abiha (wato uwa a wajen babanta)

“Ta kasance tana ji da shi da tausaya masa irin tausayin uwa ga ‘ya’yanta, tana kuma lura da shi kamar yadda uwaye mata ke lura da ‘ya’yansu kanana, wanda hakan ya zamanto abin koyi ne na tsarkakkar alakar uba (da ‘ya’yansa) wajen gina ‘ya’ya da fuskantar da ɗabi’u da rayuwarsu, da cika zukatansu da kauna da tausayi.

Haƙiƙa wannan alaƙa ta zama babbar abar misali a fagen renon ‘ya mace a musulunci da lura da ita, girmamata da ɗaukaka matsayinta. Domin karin bayani sai a duba: Hakim, mustadrak al-Sahihain, juzu’i na 4, shafi na 272 da Bukhari adabul-mufrad, shafi na 136 da abu Dauda, Sunan, juzu’i na 2, shafi na 354 da Sahih Tirmizi, juzu’i na 2, shafi na 319 da Hakim, mustadrak al-Sahihain, juzu’i na 2, shafi na 626. arbili ya fitar da shi da wasu lafuzzan a cikin kashful-gummah, juzu’i na 1, shafi na 16. da Bukhari, al-Sahiha, juzu’i na 2, shafi na 185 da ahmad xan Hambali, musnad, juzu’i na 4, shafi na 332 da Hakim, mustadrak al-Sahihain¸juzu’I na 3, shafi na 154 da ahmad ɗan Hambali, musnad, juzu’i na 4, shafi na 5; da Nasa’i, khasa’isu amirul-mu’uminina ali ɗan abu Dalib, shafi na 25 (a ciki ya zo da karin cewa: wanda kuwa ya cutar da manzon allah aikinsa ya baci) da Idan al-athir, Usudul-Gaba, juzu’I na 5, shafi na 520, da Idan abd al-Bar, al-Isti’ab, juzu’i na 2, shafi na 752.

Kaɗan daga cikin darajojinta:

Darajojin Nana Faɗima abune da babu wanda yasan haƙiƙaninsa sai Allah (S.w.T.), wane mutum ya iyakance darajojin ‘yar ma’aiki! Sai dai tare da hakan zan fadi dan gwargwadon abin da ya samu na abin da aka rawaito daga hadisan Annabi (Sallalahu alaihi wasallam).

Nana Faɗima (allah ya kara mata yarda) ta kasance mafi soyuwar ahlin annabi (Sallalahu alaihi wasallam) a wajensa. Manzon Allah (Sallalahu alaihi wasallam) ya kasance idan zai yi tafiya ƙarshen wanda zai wa yi bankwana, ita ce Nana Faɗima. kuma idan ya dawo farkon wajen da zai fara shiga wajenta ne.

Imamul Bukhari ya rawaito hadisi cewa: “manzon allah (Sallalahu alaihi wasallam) ya ce: Faɗima tsoka ce daga gareni, duk wanda ya fusata ta ya fusata ni”.

ahmad ɗan Hambali ya rawaito hadisi cewa: “Fiyayyar matayen a aljannah ita ce, Nana Faɗima” (Allah ya ƙara mata yarda).

muslim ya rawaito hadisi cewa: “Shugabar matayen mumminai ita ce Nana Faɗima” (Allah ya ƙara mata yarda).

Haka yazo a Littafin (madalimul Itratin Nabawiyya”) daga anas xan malik (allah ya kara masa yarda) ya ce: “manzon allah (Sallalahu alaihi wasallam) ya ce. Fiyayyar mataye ita ce Faɗima ‘yar Muhammadu Rasulullah, (Sallalahu alaihi wasallam) sannan asiya matar Fir’auna”.

An karɓo hadisi daga uwar muminai Nana aisha (allah ya kara mata yarda) tace da Nana Faɗima (Allah ya ƙara mata yarda): “Ba na yi miki bushara ba? Naji Manzon Allah (Sallalahu alaihi wasallam) yana cewa Shugabannin matayen gidan aljannah guda huɗu ne, sune kamar haka:

maryam ‘yar Imraan:

Faɗima ‘yar muhammadu Rasulullah, (Sallalahu alaihi wasallam)

khadija ‘yar khuwailidu.

asiya ‘yar muzahima (matar Fir’auna)’’.

An rawaito hadisi daga uwar muminai Nana aisha (Allah ya ƙara mata yarda) tace: “wata rana Nana Faɗima (Allah ya kara mata yarda) ta fuskanto tana tafiya irin na mahaifinta, sai Manzon Allah (Sallalahu alaihi wasallam) ya ce maraba da wannan ‘yar tawa. Sannan ya zaunar da ita a dama gare shi. Sai ya yi magana da ita cikin sirri sai naga tana kuka. Sai nace ya Manzon Allah (Sallalahu alaihi wasallam) zai keɓance ki da magana sannan kiyi kuka? Sai ya sake yin magana da ita cikin sirri sai tayi dariya. Sai nace, ban taba ganin farin ciki kusa da baƙin ciki ba kamar wannan rana. Sai na tambayi Faɗima akan haka. Sai tace: “ai bana faɗin sirrin manzon allah (Sallalahu alaihi wasallam) ba tunda Ransa. Nana aisha (Allah ya ƙara mata yarda) tace sai na sake tambayarta bayan wafatin Manzon Allah (Sallalahu alaihi wasallam), sannan ta cemin: “Cewa ya yi dani, mala’ika jibrilu ya kasance yana bijiromin da alkur’ani sau xaya a shekara. amma yanzu ya bijiromin dashi sau biyu a shekaran nan. wannan alamace ta ajalina ya gabato. ke ce farkon wanda zai riskeni cikin ahalina. Sai nayi kuka da jin wannan labarin. Sai manzon allah (Sallalahu alaihi wasallam) ya sake cewa dani ba kya so ki zama shugabar matayen aljannah ba.” Sai nayi dariya da jin haka.

An karbo hadisi daga abu ayyubal ansari (Allah ya ƙara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (Sallalahu alaihi wasallam) ya ce: “Idan ranar alƙiyama ta kasance, Ubangiji zai tara jama’ar farko da ƙarshe a bigire gu ɗaya. Sai mai shela ya yi shela daga cikin al’arshe (yana cewa) Ubangiji mai girma da ɗaukaka yana cewa, ku sunkuyar da kawunanku, kuma ku rintse idanuwanku. Faɗima ‘yar muhammadu (Sallalahu alaihi wasallam) za ta wuce ta kan siradi.

Dabarani ya rawaito hadisi daga Sayyadina ali (allah ya girmama fuskarsa) ya ce: “manzon allah (Sallalahu alaihi wasallam) ya ce da Nana Fadima, haqiqa Ubangiji yana azaba saboda fushinki. kuma yana rahama saboda yardarki’’.

Darul kudniy ya rawaito hadisi daga Sayyidina Abubakar (allah ya kara masa yarda) ya fada ga Nana Faɗima cewa: “Babu wani acikin halitta mafi soyuwa a gare mu kamar mahaifinki, kuma babu wani mafi soyuwa a wajenmu kamar ke bayan mahaifinki”.

Domin ƙarin bayani akan darajojin Nana Faɗima (allah ya kara mata yarda) sai a duba Hakim, mustadrak al-Sahihain, juzu’i na 4, shafi na 272 da Bukhari adabul-mufrad, shafi na 136 da abu Dauda, Sunan, juzu’i na 2, shafi na 354 da Sahih Tirmizi, juzu’i na 2, shafi na 319 da Hakim, mustadrak al-Sahihain, juzu’i na 2, shafi na 626. arbili ya fitar da shi da wasu lafuzzan a cikin kashful-gummah, juzu’i na 1, shafi na 16 da Bukhari, al-Sahih, juzu’i na 2, shafi na 185 da ahmad ɗan Hambali, musnad, juzu’i na 4, shafi na 332; da Hakim, mustadrak al-Sahihain¸juzu’I na 3, shafi na 154 da Ahmad ɗan Hambali, musnad, juzu’i na 4, shafi na 5; da Nasa’i, khasa’isu amirul-mu’uminina ali ɗan abu Dalib, shafi na 25 (a ciki ya zo da ƙarin cewa: wanda kuwa ya cutar da manzon allah aikinsa ya baci).da Idan al-athir, Usudul-Gaba, juzu’I na 5, shafi na 520, da Idan abd al-Bar, al-Isti’ab, juzu’i na 2, shafi na 752.