Netflix ya tafka asarar miliyan N250 saboda dakatar da amfani da ‘Naira Card’ da bankuna suka yi

Daga WAKILINMU

Kamfanin Netflix ya ce ya rasa mabiya 39,451 cikin kwana 40 a Nijeriya sakamakon daina amfani da katin hada-hadar kuɗi na ‘Naira Card’ da bankuna suka yi a kasar.

Bayanan da jaridar News Point Nigeria ta tattara ranar Talata su nuna cewa, kimanin ‘yan Nijeriya mabiya shafin kamfani su 39,000 ba su sabunta rijistarsu da kafar ba a tsakanin kwana 40 da suka shuɗe.

Jaridar ta ƙara da cewa, bayanan da ta samu ɗin ba su nuna yadda tsarin yake dalla-dalla ba, kawai dai an hasashen cewa asarar ta kai ta sama da Naira miliyan 250.

News Point Nigeria ta kalato da yawa daga cikin bankuna ‘yan kasuwa a ƙasar sun daina amfani da ‘naira card’ wajen hada-hadar kuɗi a matakin ƙasa da ƙasa.

Ta ce bankuna irin su Bankin Zenith da GTBank, First Bank da sauransu su ne kan gaba a wannan al’amari.

Bankunan da lamarin ya shafa sun ce ba za su ci gaba da hada-hada da wannan katin a harkar kuɗi ta ƙasa da ƙasa a intanet ba da kuma hanyoyin POS.

Sai dai sun ce har yanzu suna ta’ammali da katin Dala (Dollar Card) wajen hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa.