Ina burin a tuna ni a marubucin dake nusar da shugabanni – Gimba

“Tun Ina aji ukun firamare na ke karanta wa mutane litattafan Hausa”

Daga Abubakar M. Taheer

Dr. Hassan Gimba ƙwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru sama da 30 yana aikin jarida. Ɗan asalin garin Potiskum dake Jihar yobe, sannan mamallakin kamfanin jaridun Neptune Prime. A cikin wannan tattaunawar da ya yi da wakilinmu Abubakar M. Taheer, ya kawo irin nasarorin da ya samu a cikin aikin dama irin matsalolin da aikin na jarida yake fuskanta a yanzu. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Da farko za mu so ka gabatar mana da kanka ga masu karatunmu.

DAKTA HASSAN: Assalamu alaikum warahamatullah. Ni dai sunana Hassan Gimba haifaffen garin Potiskum dake Jihar yobe.

Tun tasowa Ina da sha’awar karance-karance tun Ina aji uku na firamare. Zan iya tunawa ‘yan’uwana da ƙannena sukan zagaye ni, Ina karanta musu littafin ‘Magana Jari’, ‘Ruwan Bagaja’ da Iliya Ɗan mai Ƙarfi’. A zamanin babu television sai dai a kunna fitilar ƙwai Ina karanto musu suna saurara.

Bayan nan dana shiga aji huɗu da biyar na firamare Ina karanta jarida, da yake mahaifinmu ɗan boko ne yakan dawo gida da jaridu kamar kowanne ɗan boko kan yi, jaridu kamar ‘Time magazine’, ‘Readers Digest’ da dai sauran su. Ni kullum yana dawowa na kan karɓa ne na karanta.

Nakan karanta jaridun daga bango zuwa bango nake karantawa. Da na shiga aji shida na kan siyi jaridun da kaina. A lokacin Idan zan tafi makaranta akan bani Sile goma, su kuma jaridun ana siyar su Sile ɗaiɗai ne.

A haka sai na siyi jaridun guda goma kala-kala Ina tahowa da su, Ina karantawa. A haka dai har ya zama na koyi karanta jarida dama na iya Turanci sosai.

Waɗanne ƙalubalai za a ce ka fuskanta ganin irin daɗewar da ka yi kana aikin na jarida?

To kasan ƙalubale kala-kala ne, kusan zan iya cewa kowa da yadda yake kallo ƙalubalai. Misali yawanci ‘yan jarida akwai fama da rashin kuɗi, wato rashin albashi don haka mutum yana ganin labari mai kyau don rashin kuɗi sai ya zama ba shi da damar zuwa ya ɗauko ba. Wani lokacin ka fita daga gida ba abinci baka da kuɗin komowa gida a haka sai ya zama mutum ya kasa ɗaukan labari. Haka kuma ada za ka rubuta labari ka ɗora a mota akai hedkwatarku, amma a yanzu za ka ga ana amfani da na’urori na zamani wanda rashin su kan hana ‘yan jaridu gudanar da aikinsu.

Da yawa daga cikin matasa suna son cimma nasara a rayuwa cikin ƙanƙanin lokaci,don haka suna kallo irinku a matsayi makwafi. Ko ya abin yake?

To a gaskiya ita rayuwa babu wani abu da ake samun sa a sama, sai anyi aiki. Yawanci waɗanda suke kallo ko suke son cimma nasara cikin ƙanƙanin lokaci suna da ƙaranci ilimin zamantakewa. Ko ɗan sarki ne baya samun sarauta sai ya yi aiki tuƙuru. Da farko sai ya koyi ilimin zama da mutane, girmama manya da kuma sanin ilimin shugabantar jama’a. Wannan ne zai ba shi dama mutane su ga ya kamata su zaɓe shi.

Duk wanda ya fara wani abu daga sama, to ba zai jima ba zai ruguje. ko kuɗi ne, sai mutum ya fara da yaron shago, kwana a ɗaki ɗaya har Allah ya yi ya zama hamshaƙin mai kuɗi. Idan malinta ce sai ka fara da ƙolonta har zuwa farfesa.

Haka shima a aikin na jarida dole za ka fara da bin manya kana koya har ya zama ka iya. Misali ka ɗauka ni, yanzu haka Ina da shekaru kusan 31 a aikin jarida.

Nasarori fa za mu su mu ji waɗanne ka samu?

To alhamdu lillah. Kasan ita nasara kowa da abinda yake kallo a matsayin nasara. Ni ta nawa janibin ta wannan aikin na yi aure na hayayyafa a aikin nake ciyar da kaina da iyayena da iyalaina dama tallafa wa marasa ƙarfi. Kuma iya gwargwado Ina gode wa Allah kan hakan.

Bayan aikin jarida kenan kana da wata gidauniya ta tallafa wa marasa ƙarfi?

Eh, alhamdu lillah, zan ce Ina da gidauniya guda biyu ta taimaka wa al’umma. Na farko Ina da gidauniya mai sunan matata wanda ta rasu sanadiyyar sanƙarar mahaifa shekaru huɗu da suka wuce, wanda muke tallafa wa masu fama da wannan cutar da ba su magani ajin farko tare da wayar musu da kai kan haɗarin cutar.

Akwai rubuce-rubuce da nake yi a jaridar Blueprint da NewNigeria da wasu jaridun ‘online’ sun kai tamanin da wani abu inda muka tattara shi rubutun ya zama littafi guda biyu. Aka ƙaddamar da su, kuɗin da aka samu yanzu haka mun fara gina asibitin masu fama da cutar kansar mahaifa.

Haka kuma Ina da gidauniya da na buɗe mai sunan Abokina Ɗan Jarida Abubakar Monja wanda muke tallafa wa iyalan ‘yan jaridun da suka rasa ransu sanadiyyar harin Boko Haram da sauran haɗarori.

A shekarar 2007 Dakta ya fara shiga harkar siyasa. Shin aikin jarida ne ya kaika wannan matsayin ko yaya lamarin ya kasance?

Eh abinda zan ce shine, a shekarar 2007 na shiga harkar siyasa gadan-gadan a lokacin da wani aminina Tijjani Musa ya yi gwamna a Yobe, ya nemi na taimaka masa inda na fito takarar sanata a Jam’iyyar AC.

Bayan wannan kuma ina ga ban sake shiga harkar siyasa ba sai dai na marawa ‘yan siyasa baya waɗanda za su tallafa wa al’umma, Ina nufi ni nakan bi mutum ne ba jam’iyyar.

A ‘yan shekarun baya- bayan nan, ka buɗe kamfanin jaridarka na ‘Neptune Prime’ da ke yaɗa labarai da ‘online’. Waɗanne nasarori za a ce an samu daga buɗewa zuwa yanzu?

To alhamdu lillah. zan iya cewa, bayan na zama ‘reporter’ a jaridu da dama kamar ‘Today Newspaper’, ‘Daily monitor’, ‘This day’ da sauran su, sai na koma gida Potiskum na yi wata jarida Informant muka samu shekaru.

Daga nan sai na koma Abuja muke buga ‘Pen Watch’ a 2008 a lokacin muna bugawa tare da ‘Leadership’ a kamfani ɗaya.

Daga nan sai na dawo ‘Leadership’ na zama edita nata, bayan zama edita daga nan minister na ‘Science and Technology’ a shekarar 2004 ya neme ni na zame masa S.A kan ‘Media and Publication’.

Daga nan na sake dawo wa Leadership Friday na zama editan inda na bar su a shekarar 2016. A shekarar 2017 a April sai na buɗe kamfanina na ‘Neptune Prime’ wanda muke watsa labarai online. Inda a bara na buɗe Neptune Prime Magazine, bana kuma muka fara talabijin na Neptune Prime.

Waɗanne abubuwa ka ke so ace al’umma ta tuna da kai da shi a matsayinka na tsohon ɗan jarida?

To alhamdu lillah, zan iya cewa kusan kowa za ka ga yana da abinda yake so ace bayan rayuwarsa an tuna da shi haka nima. Ina fatan ace wannan kamfanoni nawa na jarida ace ko bayan raina su ci gaba da gudana domin jama’a su tunani a matsayin marubuci wanda yake rubutu kan rayuwar ɗan adam da nusar da shuwagabanni yadda ya kamata su jagoranci al’ummarsu.

Wane kira ka ke da shi ga matasan ‘yan jarida da ma matasa bakiɗaya kan cimma nasara a rayuwa?

To alhamdu lillah, kira na da nake da shi ga matasa shine, su zamanto masu haƙuri. Kusan al’adar matashi shine rashin haƙuri, kusan idan ya ga wani babba yana da burin ace ya cimma sa.

Ba a samun haka sai anyi haƙuri an kuma yi aiki tuƙuru yau da gobe ana samun shekaru har Allah Ya kai ka kan wannan matsayin.

Idan ka duba za ka ga wani ya ɗauki shekaru 20, 30 waje cimma nasararsa, amma matashi kullum ya rinqa tashi da jin cewa, yana son yin daidai wannan. Haƙuri da jajircewa na taimaka wa wajen cimma nasara a rayuwa.

Aikin jarida yana fuskantar barazana sakamakon bayyanar kafafen sada zumunta. Wane kira ka ke da shi musamman ga ‘yan jarida kan aikinsu?

To a yanzu gaskiya sakamakon bayyanar kafafen sada zumunta da mutum ya samu data shima ya zama ɗan jarida. Wanda kuma lallai ba haka abin yake ba, aikin jarida aiki ne da yake da tsari yake da manufofi ba kamar na sada zumunta ba.

To dole ɗan jarida ya zama yana kan wannan tsari domin ya bambanta da ɗan ‘social media’. Ya zama yana rubutu domin ƙaruwar al’ummarsa da ma duniya bakiɗaya.