Zargin miliyan N99: Kotu ta ɗaure alƙali da mataimakansa a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Kotun Majistare mai lamba 14 ta aike da wani alƙali da ma’aikatansa na Hukumar Shari’a kurkuku saboda zargin su da wawure Naira miliyan 99.

Mai Shari’a Mustapha Sa’ad Datti ya aike da mutanen ne bisa zargin su da yin sama da faɗi da kuɗaɗen wasu marayu.

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ce ta gurfanar da waɗanda ake zargin gaban kotun.

Sani Ali, Sani Uba Ali, Bashir Baffa, Gazzali Wada na daga cikin waɗanda ake tuhuma.

Sauran sun haɗa da Hadi Tijjani Mu’azu, Alkasim Abdullahi tare da Yusuf Abdullahi, Mustafah Bala, da Ja’afar Ahmad, Adamu Balarabe, da kuma Aminu Abdulhadi.

Sai kuma Abdullahi Sulaiman Zango, Garba Yusuf da Bashir Ali Kurawa tare da Usaina Imam.

Ƙarar ta nuna ana tuhumar waɗanda lamarin ya shafa ne da laifin haɗa kai da cin amana da satar Naira miliyan 99.

Waɗanda ake zargin duk sun musanta laifukan bayan karanta musu.

Barista Zaharaddin Kofar Mata, shi ne mai gabatar da ƙara, ya roƙi kotun da ta sanya wata ranar domin sake gabatar da shaida.

A nasu ɓangaren, lauyoyin waɗanda ake kara sun nemi Alƙalin kotun ya ba su beli amma ya ƙi amsa wa buƙatarsu.

A ƙarshe, Alƙalin ya ɗage shari’ar zuwa ran 1 ga Fabrairun 2023, inda kotu za ta bayyana matsayinta game da roƙon belin da aka yi mata.