Yaƙin Tabuka da hikimar adabin baka

Daga SHEHU SANI LERE

Yaƙin Tabuka, yaƙi ne da ba a kai ga yin sa ba, amma hikimar baka, ta sanya wani makaho a Arewacin Nijeriya (Na mance sunansa) tsaya wa ya shirya karatu cikin sigar waƙe da kalmomi majeranta masu bibiyar juna masu daɗin ji da saurare ga duk wanda a ke rera wa a gabansa.

waƙar ta shahara a Ƙasar Hausa, ta yadda har kasa-kasan karatun a ke saida wa, a riqa saurara ana girgiza kai wasu na zibda hawaye.

Haziƙin ya fi mai da hankali wajen fito da sadaukantakar Imamu Ali a cikin waƙen, ta yadda ya nuna shi a matsayin zakaran cin galabar yaƙin a kan mushirikai.

Ya kuma nuna irin ƙarfin hali irin na kafuran waccan lokaci wajen tsaya wa ƙyam! ba gudu ba ja da baya a kan kafircinsu a inda ya nuna yadda Sarkin Tabukar ya yi fushi mai tsanani a yayin da ya samu labarin Musulmai sun yi alwala da ruwan Tafkin Tabuka, a ganinsa wannan ba ƙaramin gazawa ba ce a wurinsu su yarda a taɓa musu ruwa har a yi alwala.

Haziƙin ya yi amfani da kambamin zulaƙe wajen yaba wa ɗangarorin biyu. A ƙoƙarin yaba wa Sayyadi Ali da fito da jarumtarsa sarari ya nuna:

1- ya biyo iska a guje da nufin sare mata kai saboda ta yi iƙrararin zuwa ta yi masa ƙarya, sai da manzon Rahama ya cece ta. Da ya sare mata kai tun a waccan lokaci da ba mu san wacce iska zamu shaƙa yanzu ba.

2- A ƙoƙarin gwada ƙarfin dokin da zai tafi yaƙi da shi, sai da ya tsistsinka dawakan madina kakaf! Bai sami mai ƙarfin da zai iya ɗaukarsa ba.

3- An kasa ɗaura masa sulke a jikinsa saboda gashin jikinsa na yayyanka masu ɗaura masa hannu, sai da wata tsohuwa ta ce tana bin sa kuɗin daddawa.

4- Dawakan duniya sun kasa ɗaukarsa sai da aka zo da doki daga sama, shi ma kuma ya saɗa shi a wuya saboda ya raina hanzarinsa.

5- A lokacin yaqin, idan ya kai sara dama yana kashe 1000, hagu 1000, gaba 1000, baya 1000.

6- Dokinsa ya kan taka 1000, ya hankaɗe 1000, ya ture 1000, da dai sauransu.

an yi amfani da salo na jan hankali tare da sanya wa mai sauraro kwaɗayi. Allah Ya jiƙan mawaƙin.