Iyaye su ba wa ‘ya’yansu mata damar kawo koken gidan aurensu – Saratu G. Abdul

“Kada iyaye su fake da rumfar talauci, su yi biris da tarbiyyar ‘ya’yansu”

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga ABUBAKAR M. TAHEER

A satin da ya gabata, idan mai karatu zai iya tunawa, mun faro firarmu da ƙwararriya a ɓangaren matsalolin ƙwaƙwalwa, Hajiya Saratu G. Abdul, inda muka yi shimfiɗa da sanin ita kanta ko wacce ce, tarihi zuwa aikin da ta ke yi har zuwa abinda ta fuskata a yanzu. Daga nan muka gangara kan haɗa ku da ilimin da ta kwankwaɗa ta ɓangaren ciwon ƙwaƙwalwa da kuma irin tasirin sa. A kan wannan matsalar ce muka dasa aya tare da alƙawarin ci gaba a wannan sati. Idan kun shirya, mu fara da tambayar da muka kwana kanta a makon da ya wuce:

MANHAJA: Ko akwai wani taimako da ya kamata likitocin su yi wa makusantan masu lalurar ƙwaƙwalwa ta fuskar wayar da kai?

SARATU G: Ƙwarai likitoci ke iya bada taimako ta wannan ɓangare, domin ta sanadiyyar wayar masu da kai kan ita kanta nau’in cutar ta ƙwaƙwalwa da majinyacin ke fama da ita zai taimaka wurin fahimtar sa, kuma ta wannan hanya ce za su iya gane hanyoyin da ya kamata su bi don sama masa sauƙi da kuma yadda za su yi rayuwa tare da shi cikin jin daɗi.

Waɗanne hanyoyi ki ke ganin gwamnati za ta bi wajen bada gudunmuwa ga masu wannan matsala don ganin sun samu waraka?

Gwamnati tana da nata gudunmawar da zata bada wajen ganin an rage yawaitar masu matsalar ƙwaƙwalwa. Kamar tsara gangami na wayar da kai, wato ‘awareness’, inda za a wayarwa mutane kai su gane cewa, matsalar ƙwaƙwalwa kamar zazzaɓi ko ciwon kai ta ke, kuma ana samun sauƙi. Sannan su samar da ƙwararrun likitoci da suka ƙware a ɓangaren, don ba wa masu fama da matsalar damar samun sauƙi ta fuskar magani. Sannan kuma gwamnati ta samar da asibitoci na musamman da ke magance wannan matsala tare da samar da guraben shan magani na tafi-da-gidanka.

Bari in baka misali da nan Turai, da zaran ka ji alamu na irin wannan matsala, akwai wuraren da za ka garzaya, a bincike ka, idan matsalar ƙwaƙalwa ce, a baka magani a take.

Sannan a ɓangare ɗaya, hukumomi su ƙara ƙaimi wurin ganin sun magance matsalar shigo da miyagun ƙwayoyi, hakan zai kawo ƙarancin masu shaye-shaye, wanda hakan zai magance masu faɗawa a cutar ta ƙwaƙwalwa a wannan sanadi.

Baya ga gamnati su wa ki ke ganin za su iya bayar da gudunmawa ta wannan ɓanagare?

Masu hannu da shuni su ma suna da gudunmawa da za su iya bayarwa a matsala ta jinyar ƙwaƙwalwa, musamman ma idan ka yi duba da cewa, lokuta da dama talauci ne ke zama silar matsalar ƙwaƙwalwa da kuma rashin aikin yi.

Don haka su samar da kamfanoni da zai ba wa mutane damar samun abin yi, hakan zai ɗebe masu kewa, kuma zai iya zama siraɗin da zai iya tsallakar da su daga fafawa wannan cuta ta ƙwaƙwalwa. Yawanci rashin abin yi na sa ƙwaƙwalwa ta riƙa tunani marar kyau, wanda zai iya kai mutum ga irin wannan matsala.

Kuma ya kamata masu kuɗi su rinƙa taimaka wa yara masu ƙwaƙwalwa, waɗanda ke da burin yin karatu, su biya masu kuɗin karatun don samun cikar burinsu, rashin yin hakan zai iya jefa yaran a mawuyacin hali na damuwa.

Idan muka duba kuma ta ɓangaren matsalar shaye-shaye, kaga ai matsala ce da ke da alaƙa da ƙwaƙwalwa. Ta ɓangare ɗaya idan ka duba yadda ‘yan siyasa ke amfani da wannan damar ta hanyar janyo ire-iren waɗannan yara da suka samu kansu a matsala ta shaye-shaye, su dinga siya masu kayan maye don yin hauragiya a lokacin siyasa.

Kuma abin takaici idan ka duba, kaso mai yawa na yaran talauci ne ya yi sanadin samun kansu a wannan hali. Iyaye ba su da abin yi, don haka ba su sa su a makaranta ba, su kuma damuwa da zaman banza tare da cuɗanya da kowaɗanne irin mutane ya sa suka koyo ɗabi’ar ta shaye-shaye, kuma abin a ce su ‘yan siyasar su taimaka masu wurin tsamo su daga wannan fitinar, a’a sai dai ma su ƙara rura wutar ta hanyar wadata su da kayan mayen.

Daga ƙarshe zan yi kira ga iyaye da su saka ido ƙwarai da gaske kan mu’ammalar ‘ya’yansu, domin dai sai ka tashi ne Allah zai taimake ka. Kada ku fake a rumfar talauci ku yi biris da tarbiyyar ‘ya’yanku, domin ku ya kamata ace kun saka ido kafin duk wani taimako da ya kamata gwamnati ko masu hannu da shuni su yi ma ku. Shaye-shaye ya zama ruwan dare, kuma haƙƙi ne naku ku iyaye da ku yi mai yiwa wurin ganin kun ba wa ‘ya’yanku kariya daga faɗawa cikin sa.

A ɓangaren ‘ya’ya mata da a baya ba a cika samun matsala ta shaye-shaye a cikin su ba, musamman nan gida Nijeriya. Shin me ke kawo yawaitar mashaya a mata?

Ee to ‘ya’ya mata ma suna samun ‘problem’ waɗanda ka iya haifar musu da matsala ta ƙwaƙwalwa, ba wai shaye-shayen kai tsaye ke haifar masu da matsalar ba. A kan samu wasu canje-canje ne a jiki, wato ‘chemical process’ waɗansu sinadarai da zasu iya haifar ma ƙwaƙwalwa matsala.

Idan mace ta samu kanta a ƙunci a zamntakewarta da mijinta, ma’ana yana muzguna mata. Shin waɗanne irin matakai ya kamata ta bi don guje wa matsalar damuwa da zata iya kaita ga aikata mummunan nufi ga shi mijin nata?

Idan mace ta samu kanta a zamantakewa ya zama mijinta na muzguna mata, da farko, iyaye su ba wa ‘ya’yansu dama cewa, bayan aurar da su sanin suna da dama ta sanar da iyayensu halin da suke ciki wanda za ka ga mu a al’adar malam bahaushe babu wannan damar.

Ko ince babu wannan sakewar, za ka ga idan yarinya an aurar da ita, koda tana fuskantar matsala a cikin gidanta saboda al’ada da kuma ɗabi’ar bahaushe mace bazata iya zuwa ta tunkari iyayenta ta sanar da su halin da ta ke a ciki ba.

Wani lokacin idan ta zo ta faɗa musu zai zama iyaye sun bata haƙuri ta rufawa kanta asiri ta koma gidan mijinta, gara ace tana gidan mijin nata kowanne hali ta ke ciki ta yi haƙuri saboda kar ta zama ƙaramar bazarawa. Gaskiya wannan ba daidai ba ne, saboda mu sani ‘ya’yanmu kiwo ne aka bamu, kuma za a tambaye mu kan wannan kiwon.

Bawai ka ba wa ɗanka abinci, sutura, ilimi da sauransu shi ne kawai ba, a’a hatta lafiyar ƙwaƙwalwarsa haƙƙi ne dake a wuyanka ka kula masa da shi.

Idan ya zama ba ta jin daɗin zaman auratayya, kamata ya yi iyaye su ce, da ta samu matsalar ƙwaƙwalwa gwara ta zama bazawara. Iyaye su shigo ciki su raba auren, sabodaa matsala ce babba ace a ci gaba da fuskantar matsalar idan sun fuskanci babba ce. Iyaye su bama yaransu dama wajen su sanar da su duk halin da suke a ciki. Ba mafita ce ba a bar yarinya da wannan cutar ta damunta.

A ɓangare ɗaya akwai matan da dama da suke kashe mazajensu ba don rashin kyautatawa ba, sai don kawai za a yi masu kishiya. Shin su ma suna daga cikin masu matsalar ta ciwon damuwa?

Ee to a gaskiya baɗan ce matan dake kashe mazajensu saboda za a mu su kishiya suna da matsalar ƙwaƙwalwa ba.

Abinda mutum ya ƙuduri aniyar zai yi ba yana nuna yana da cutar ba ne, abinda nake tunani shi ne, mutum wanda yake da lafiyayyar ƙwaƙwalwa ba zai ɗauki matakin hallaka wani makusancinsa a cikin hayyacinsa. Amma wannan ba hujja ba ce ta cewa, wadda ta aikata hakan tana fama da cutar.

Ba za mu allaqanta duk abinda ya faru a rayuwa ɗan Adam da jinyar ƙwaƙwalwa ba. Kamar yadda na faɗa maka a baya, ita kanta jinyar ba wai mutum ne kai tsaye zai ce yana fama da jinyar ba, dole sai ya je asibiti anyi gwaja-gwaje, tambayoyi, bincike-bincike da dai sauran su. So a gaskiya ba zan ce matan dake kashe mazajensu suna fama da cutar ba a kai tsaye ba, zai iya zama haka, zai kuma iya zama ba haka ba ne. Bincike ne zai tabbatar da hakan.

Daga ƙarshe za mu so ki ba wa mata ‘yan’uwamki shawara a ɓanagare biyu, wato sahye-shaye da kuma ita kanta matsalar ƙwaƙwalwa da ta shafi damuwa da suke cin karo da ita a zaman aure?

So a ƙarshe kiran da nake da shi ga ‘yan’uwana mata shi ne, duk wanda yake shiga cikin al’umma a yanzu ya san akwai matsalar shaye-shaye da ta vulla cikin mata, bawai ‘yan mata ba har da matan aure a gidajensu, gidan biki a zuba ƙwaya a abin sha da ake rabawa a sha,a samu yanayi da yin maye domin shagala. To lalle mata su sani shaye-shaye ba ya da wani amfani.

Sannan kuma duk irin damuwa da mace za ta samu kanta a cikin gidan miji ne ko kasuwanci, ta sani shaye-shaye ba shine maslaha ga abin da ke damunta ba. Akwai hanyoyi da za ta bi wajen magance wannan matsalar. Sannan za ka ga matan da ke fuskantar matsalar damuwa ana alaƙanta su da hauka.

Lalle matsalar ƙwaƙwalwa jinya ce kamar zazzaɓi, ciwon ciki da makamantan su, yadda za ka je asibiti ka nemi magani kaga ƙwararren likita haka ita ma za ta je taga likita. Ya ba ka magani ka kuma warke.

Idan mace ta samu matsala a zamantakewa ta yi ƙoƙari ta fito da abinda yake damunta ta faɗawa iyayenta ko likitanta. Ba wai magani ba likita zai bata shawarar yadda zata yi wajen magance damuwa. Saboda barin damuwar a ciki illa ce ba kaɗan ba. Amma da zarar an fitar da ita za a samu sauƙi. Kuma akwai abubuwa da ya kamata mata su rinƙa yi kamar cire damuwa komin ƙanƙantarta. Haka kuma mata su rinƙa cin abinci mai gina jiki, ganye da sauransu da kuma yawan motsa jiki shi ma yana magance matsalar.

Madalla. Mun gode.

Ni ma na gode ƙwarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *