Siyasar bana: Kada mu sake mu yi zaɓen tumun dare

Daga BELLO MUHAMMAD SHARAƊA

Zuwa ga talakawa masu zaɓe. Wannan siyasar da muke yi, Allah ya sani kuma wasu jama’a da muke tare da su, sun san haka, masu fahimta daga lafuzanmu za su gane, niyyarmu da burinmu shi ne yadda sauran al’umma suke amfanar da rayuwarsu ta hanyar ingantaccen tsari na ƙasa, haka muke fata a samu a Nijeriya, a nan duniya mu yi abin kirki, na ƙwarai da alheri, a lahira mu karɓi sakamako a hannun dama.

Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta tsara a duk faɗin Najeriya za ta riƙa ba da bayanai duk sati biyu, daga nan zai koma duk sati, a wannan shekarar shekara sabuwa da aka shiga kuma, za su riƙa irin waɗannan bayanan a kullum har ranar zaɓe. Tun ranar 28 ga Satumba aka buɗe kamfen na masu neman shugabancin ƙasa da masu neman wakilci a majalisar dattijai da tarayya. An buɗe ƙofa na masu neman gwamnoni da majalisar jiha.

Ma’anar sanya wannan rana shi ne, a bai wa masu neman mulki dama su kewaya gurin jama’arsu, su mu’amalancesu, su gaya musu jam’iyyunmu sun tsaida mu, mu wakilcesu, muna son ku bamu goyon baya, ku zaɓe mu, ga tsarin da za mu aiwatar don amfaninku da wasarmu idan Allah ya kai mu ga nasara.

A ɗan taƙadirin sabgar siyasa da na shiga a SDP a shekarun 1992-3 da GDM a zamanin Abacha da PDP da APC a wannan jamhuriyya da muke ciki, idan irin wannan lokacin ya zo, hukumar zave ta buɗe ƙofa, to fa sai ka ga lokaci ne na amfani da kuɗi, lokaci ne na samun cinikin masu sayar da makamai na gargajiya, lokaci ne na baje kolin miyagun ƙwayoyi da kayan maye, lokaci ne na cin mutuncin juna, lokaci ne na ganganci, lokaci ne na rashin kunya da fargaba, lokaci ne na rigima da ta da tarzoma, wannan shi ne lokacin kakar kisa da sara da suka.

A yawon dana yi na kamfen a tsawon wannan lokaci waɗanda ake amfani da su a wannan lokacin yara ne matasa, akasarinsu ‘ya’yan marasa galihu. Jefi-jefi, ‘ya’yan masu galihu suna shigowa a yi da su, amma fa su suna zuwa a cikin yanayi mai kyau da tsaro da aminci da kamun kai, kuma suna zuwa ne a ‘yan kallo. A cikin matasan za ka gane ‘yan jagaliya, su suna zuwa a abin hawa gama-gari, wanda inda lamura suna tafiya yadda ya kamata a ƙasar nan, irin waɗannan ababen hawa ko dabba ba za a ɗauka da su ba, ballantana ɗan adam. Su kuma ‘yan gatan suna zuwa a lafiyayyun abin hawa, na zamani, na gani na faɗa.

Wallahi na sha gani a irin tarukanmu na siyasa an yi sara, an yi suka, an yi kisa. Da idona na ga an kasa tabar wiwi da ƙwayar rochi da man sholisho da ƙunshin giya a fai-fai ana talla kuma ana siya, a filin taron siyasa, za ka ga ana kunnawa a zuƙa ko a sha. Ba irin makamin da ban gani ba, wani ma ban san sunansa ba. Za ka ga gariyo da adda da takobi har da wani wai shi fate-fate da tsitaka da barandami da manyan wuƙaƙe da ƙaho har na mariri.

Abin ta’ajibi ban taɓa ganin ‘ya’yan manyan nan namu ba, ɗauke da makamin ba ko kayan mayen. Ina dai ganinsu da kuɗi, kuma suna rabawa, iyayen nasu kuma ni dai a gabana ban tava ji sun yi Allah wadarai da wannan tsarin ba, a ɓoye ko a sarari.

Wannan shi ne abin da ya ke damu na ƙwarai. Na kalli yadda ‘yan siyasar Turai da Amurka da ƙasashen Asiya suke yi, sam ba haka suke ba. Akwai tsabta da ilimi da girma da arziki da ‘yanci da abin sha’awa. A Afirka ne da Latin Amurka ake wannan shirmen da aikin kawai.

Yana daga cikin burina a ƙoƙon zuciyata in na samu dama sai na jagoranci yaƙi da wannan tsarin banza da wofi da yake lalata mana shugabannin yau da gobe. Ba wani abu ne da ya gagara ba, na san yana da wahala, in dai muka sami iko wallahi sai mun yaƙe shi ta kowacce fuska. Sai an daina da yardar Allah.

Yanzu da babu wata dama a hannunmu, duk da haka za mu yaqi wannan abin da iya karfin da muke da shi na yau. Muna siyasa ne domin al’ummarmu ta zama abar misali nagari, ba abar tozartawa ba, kuma koma baya. Sai an soke daba da jagaliya ta hanyar yaƙar jahilci da talauci. Duk mai neman mulki da zai ɗaure gindin wannan tsarin, kar mu yi shi kuma kar mu bi shi.

Sharaɗa ɗan siyasa ne kuma ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto ne daga Kano.