Tsadar karatun jami’a ba abin zolayar ɗalibai ba ne

Daga IBRAHYM A. EL-KHALIL

Game da qarin kuɗin makarantun jami’o’i da Gwamnatin Nijeriya ta yi.

In dai school fees ya koma 200K, 300K, mutum ba zai nemi digiri na biyu (MBBS) ka ba shi darasin kayan tarihi (Archeology) kuma ya karɓi ‘Archeology’ ɗin ya yi ba.

Ba raina darasin kowa nake ba saboda na san babu ilimin da ake rainawa. Amma a lura, tsadar jami’a zai sa a dena karanta wasu darussan sosai. Duk darasin da ba wai ana amfani da shi ba ne a nemi kuɗi, to kamar fa iyaye/ɗalibai ba za su zuba “hannun jari” a darasin ba.

Boko Sana’a ne. Hatta Boko Aqida sun san wannan sarai, kawai dai wasan jika da kaka ne suke yi da mu. Boko harka ce ta morar rabonka na duniya ko dai ta fannin kuɗi, ko mulki, ko sharafi, ko dai haka kawai don nishadi da wasa ƙwaƙwalwa. Shi ya sa boko ya zama halas a musulinci. Bai zama wajibi ba, bai kuma zama haramun ba.

To kasancewarsa sana’a, idan fa jari (school fees) ya yi yawa, dole mutum zai sa ido wajen samun gwaggwaviyar riba, “return on investment” (ROI). Wato riba kenan a taƙaice.

Shi ya sa in dai kuɗin makaranta da gaske a dubu 150 zuwa dubu 250 zai kasance, to haƙiƙa wasu sassan ilimin za su fara fuskantar barazana saboda ba za su samu ɗalibai ba ba. Domin a Najeriya waɗannan darussan ba su da hanyar samun kuɗin a cikinsu, kamar yadda suke da shi a wasu ƙasashen.

Don haka, duk wanda aka ba wa ya karanci darasin, idan ya zauna ya lissafa kuɗin makaranta, sai ya hango cewa a Nijeriya fa darasin ba shi da ƙima sosai a kasuwa, to sai ya ajiye darasin ya ce zai nemi wani daban wanda yake da ƙima a kasuwa.

Na sha duba jadawalin zaɓar darussa na makarantun koyon kasuwanci na duniya. Tun daga kundin za ka ga suna maka wani ɓoyayyen talla game da cewa fa ga ƙiyasin kason samun ayyuka na masu digirinsu.

Misali INSEAD MBA, sai su ce maka kaso 92% na waɗanda suka kammala darasin a jami’a sun samu aiki a cikin watanni uku da kammalawa, kuma ba ƙarya suke ba, hakan ne.

To daga lokacin da farashin karatun boko zai yi tashin gwauron zabi a Nijeriya, kamar fa duk darasin da bashi da irin wannansamun kuɗin ko aiki, gaskiya zai yi kuka da rashin ɗalibai. Rashin ɗalibai kuwa ma’anarsa shi ne sashen koyon darasin ya mutu murus kenan, ba zai kai labari ba.

El-Khalil ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto ne daga Ƙaramar Hukumar Zariya, da ke Jihar Kaduna.