Kamar kumbo, kamar katanta: Kamar Abba, kamar Gawuna

Daga FATUHU MUSTAFA

Ina mamakin masu yaɗa batun Gawuna wai ya ce zai ɗora daga inda Ganduje ya tsaya. A magana ta gaskiya idan aka kalli manyan yan takarar Gwamnan Kano, za a ga kusan salon kamfen nasu iri ɗaya ne, kawai alqawurra ne suka banbanta. Ga wasu misalai kamar haka:

  • Dukkansu kyanwar Lami ne, ba cizo ba kama vera. Kowanne ya haƙƙaƙe zai ci zaɓe ne, saboda ƙarfin ubanɗakinsa da ya tsayar da shi.

Ba wanda ya yadda ya jagorancin tafiyar takararsa, kowanne ubanɗakinsa ne ke magana da yawunsa. Kafin ka ji Abba ya ce “A” sai ka ji an ce Kwankwaso ya yi magana sau dubu.

Ba wanda ya nuna zan zo da wani sabon abu Kano, kowanne maganar zai dora daga inda ubanɗakinsa ya tsaya yake.

A lokacin da ake maganar kawo sauyi a fannin noma, tattalin arziki da masana’antu, har yanzu a Kano, mu maganar tura yara ƙasashen waje muke su je su yi karatu, su dawo ba aikin yi. Me muke musu tanadi su yi, idan sun gama karatun? Shin samun satifiket kawai ya isa, ko sai an haɗa da abinda za a yi aiki da karatun? Kar fa mu manta, amfanin ilmi aiki da shi.

Shin mu kuma namu makarantun irin su Jamiar Wudil da ta Maitama Sule haka za su yi ta zama, ba cigaba? Sai dai mu kwashi kuɗi mu raya na waje!

Yaushe yan takarar Gwamnan Kano za su fara maganar hanyoyin da za su bi domin haɓaka aikin gona, da farfaɗo da masana’antu a Kano? Ba sa ganin lokaci ya yi da za su fara tunanin samar wa matasa aikin yi ta wata hanyar ba aikin gwamnati ba?!

Ina batun yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da ya yi wa matasan Kano katutu? Me za su yi su shawo kan batun yawaitar daba da fyaɗe dake addabar mutanen Kano? Ina batun yashe madatsun ruwa 13 da haɓaka noman rani a jihar Kano? Shin sai yaushe Kano za ta dawo daga rakiyar jiran rarar man fetur a ƙarshen wata?

Ni dai ina ganin, akwai buƙatar mu zauna mu sake lale. Amma wannan tsarin na zan muku famfon fura da nono, ba zai kai mu ko ina ba.

Allah ya taimake mu, Ya ba mu jagorori nagari.

Fatuhu ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto ne daga Abuja.