Yadda ‘yan siyasa ke barazana ga sarautun gargajiya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A baya na taɓa yin wani rubutu mai kama da wannan, kuma a wannan shafi da ke tsokaci kan al’amuran yau da kullum, inda na nuna irin ƙalubalen da masu masarautun gargajiya ke fuskanta a hannun ‘yan siyasa da masu mulki. To, abubuwa dai sai cigaba suke yi, ana cigaba da warware rawunan wasu sarakuna da masu riƙe da sarautun gargajiya saboda dalilai na siyasa.

Sarakuna da dama na cikin zaman ɗar-ɗar saboda makomar rawanin su, musamman a jihohin da aka raba gari tsakanin jam’iyyar da Gwamna ke yi da kuma jam’iyyar da aka fahimci Sarki ko wani babban mai riqe da sarauta na jihar yana ra’ayi. Wasu sarakunan ma an mayar da su na jeka na yi ka, saboda ba a shigar da su cikin wasu al’amuran gwamnati kuma ba a tafi da su yadda tsarin al’adar sarautun gargajiya suke a Arewacin ƙasar nan, saboda an samu kuskuren inda Sarki ya juyawa jam’iyya mai mulki baya. Kai, a wasu jihohin ma ƙiriƙiri Gwamna ko muƙarrabansa suke yi wa sarakunan jihar barazana kan ko dai su bi tsarin abin da gwamnatin jiha ko ta tarayya take kai ko kuma a bakin rawaninsu.

Rahoto na baya bayan nan shi ne batun tuve rawanin tsohon Wazirin Bauchi Alhaji Muhammadu Bello Kirfi, wanda aka yi zargin yana da alaƙa da batun siyasa. Kodayake wannan ba shi ne karon farko da ake sauke tsohon Wazirin ba, amma a wannan karon ana ganin akwai batun yadda yake bayyana ra’ayinsa game da siyasar Bauchi da alaqar sa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar neman kujerar shugabancin ƙasar nan a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Jaridar Daily Trust ta ranar 5 ga watan Janairu, 2023 ta rawaito cewa, tuɓe tsohon Wazirin Bauchi na da nasaba ne da wani taron manyan muƙarrabansa da ya kira daga dukkan sassan Jihar Bauchi, waɗanda suka hallara a gidansa, domin tattauna yadda za a tarbi tawagar yaƙin neman zaven Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP, da ke shirin zuwa Bauchi, wanda kuma ake zargin akwai rashin jituwa tsakanin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar da Gwamnan Jihar Bauchi, Abdulƙadir Bala Muhammad.

Sai dai kuma wata majiya ta shaidar da cewa tun lokacin da Gwamnan jihar ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar neman shugaban ƙasa a Jam’iyyar PDP, kuma ya nemi shawarar tsohon Wazirin Bauchi, shi kuma ya nemi da ya haƙura sai nan gaba, don a bai wa Atiku Abubakar wannan damar, kasancewarsa na hannun daman Atiku, aka fara samun rashin jituwa a tsakanin vangarorin biyu.

Don haka ko a wasiƙar sauke Wazirin da Sakataren Masarautar Bauchi, Alhaji Shehu Mudi Muhammad ya sanyawa hannu, aka ce an tuve rawaninsa na wazirci ne da kasancewarsa mamba a a Majalisar Masarautar Bauchi, saboda kalamansa na rashin girmamawa ga Gwamnan jihar. Kwatankwacin irin hujjojin da aka bayar sauke tsohon Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, lokacin da shi ma ya samu takun saƙa tsakaninsa da Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a shekarar 2020.

Tsige sarakunan gargajiya a Nijeriya abu ne wanda aka daɗe ana yi tun bayan samun ’yancin ƙasa daga hannun turawan mulkin mallaka. Haka kuma tun dawowar dimukraɗiyya a 1999, saɓani, rashin jituwa musamman na siyasa ya yi sanadin cire rawanin wasu Sarakuna a Arewa da ma kudancin ƙasar nan.

Kuma ba ni kaɗai ba, da dama manazarta da masu nazarin al’amuran yau da kullum sun yi ta bayyana buƙatar muhimmancin samar wa sarakunan gargajiya matsayi na musamman a kundin tsarin mulkin ƙasa, domin kare martabar rawunan su, da kara musu kima da daraja. Ta yadda zai yi wuya wani Gwamna ko shugaban Ƙaramar Hukuma ya ce zai tsige Sarki ko ya tozarta shi, saboda saɓanin siyasa ko ra’ayi.

Abin takaici ne sosai yadda aka mayar da rawanin sarakunan mu na gargajiya, iyayen ƙasa ya zama abin wulaƙanta da cin mutunci. Masarautun da ke da ɗimbin tarihi na addini da na al’ada, wanda suke da ƙarfin faɗa a ji da tasiri a wajen talakawansu, an mayar da rawunan su abin ƙasƙantarwa.

Halin da sarakunan mu na gargajiya suke ciki a wasu sassan ƙasar abin tausayi ne da takaici. An bar su da tuma tuman rawani amma babu ƙarfin iko ko wani aiki na musamman da suke gudanarwa a hukumance. Hatta albashin da ake ɗan yaga musu daga ƙananan hukumominsu bai taka kara ya karya ba.

Yadda wasu gwamnonin ƙasar nan suke kallon sarakuna kamar nauyi abin wulaƙantarwa marasa gata ya sa kima da darajar sarautar na zubewa a idanun wasu ‘yan ƙasa, saboda takaicin abubuwan da suke ganin na faruwa kan waɗanda suka riqa a matsayin iyayen ƙasa. Dubi dai abin da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya yi a shekarar 2017 lokacin da ya tsige Hakimai 313 da masu unguwanni 4, 453 a yunƙurinsa na yi wa masarautun da ke Jihar Kaduna garambuwal.

Nasir El-Rufai ya ce wai kuɗaɗen da waɗannan Sarakuna suke ci ya yi yawa, don haka ya tunvuke su, domin gwamnati ta samu kuɗin da za ta yi wa al’umma aiki. Ko a baya bayan nan ma cikin shekarar da ta gabata, Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle, Zamfara, ya cire Sarkin Zurmi, Abubakar Atiku, Sarkin Dansadau, Hussaini Umar, da Sulaiman Ibrahim, Dagacin Birnin Tsaba bisa zargin sakaci da harkokin tsaro da kuma haɗa kai da ‘yan bindiga.

Haka ma, a shekarar 2020 Gwamnan Jihar Anambra Willie Obiano ya tsige sarakunan gargajiya 12 da suka haɗa Igwe Chijioke Nwankwo na Nawfia, da Igwe Anthony Onyekwere na Owelle, da Igwe G. B. C. Mbakwe na Abacha, bisa zargin sun raka Yarima Arthur Eze zuwa Abuja Don ganawa da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Haka shi ma Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ya yi barazanar tsige wasu sarakunan gargajiya da ke jihar sa saboda rashin samun halartar taron majalisar sarakunan jihar, da zargin da yake yi na nuna wa gwamnati tsaurin ido.

Ya ce, babu wani basarake da ke saman gwamnati, dole kowanne sarki ya yi biyayya ga abin da gwamnatin lokacinsa ke so. Kamar yadda a baya ya sha faɗa cewa, bai amince wani basarake ya shiga siyasar adawa da gwamnati ba.

Ya kamata gwamnati da ’yan majalisu su samar da wasu dokoki da za su fitar da matsayin sarakuna da martabarsu a cikin kundin tsarin mulkin ƙasa, don su samu bakin magana a hukumance, kuma su samu ƙarfin iko na zartar da wasu ayyuka da suka shafi cigaban jama’ar su.

Mu kuma a namu ɓangaren talakawa, ya kamata mu zama masu girmama sarakunan mu, da manyan ƙasa, tare da ba su kulawar da ta kamata, a matsayin su na manyan ƙasa, ma’abota adana tarihi da sanin darajar ƙasa. Mu sani a halin da ƙasa ke ciki, sarakunan mu ba su da wani ƙarfin ikon juya wani abu, ko sanya wa a yi dole, sai dai suna da bakin magana da isar da saƙon talakawa zuwa ga zaɓaɓɓun shugabanninsu.