Yau Emefiele zai bayyana gaban kotu kan badaƙalar Dala miliyan 53

Daga WAKILINMU

A wannan Larabar ake sa ran Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, zai bayyana a gaban Babbar Kotun Abuja dangane da shari’ar sama da Dalar Amurka miliyan 53 na kudaden ‘Paris Club’.

A wata ƙara da aka shigar gaban kotun ranar 20 ga watan Oktoban 2022, Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya bai wa Emefiele odar ya bayyana a gaban kotun ran 18 ga Janairu don sauraron shari’ar.

Umarnin kotun ya biyo bayan ƙarar da lauya Joe Agi, ya shigar ne kan kamfanin Linas International Ltd da Ministar Kudi da CBN ta hannun lauyoyinsa, Isaac Ekpa da Chinonso Obasi.

A cikin karar, yana neman kotu ta bai wa Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda odar cafke Emefiele da lauyoyinsa tare da gabatar da su ga kotu.

Ƙarar ta taso ne kan hukuncin Dala miliyan 70 da aka yanke wa Linas kan ayyukan lauyoyi game da kuɗin Paris Club, wanda aka ce Emefiele ya saki Dala miliyan 17 sannan Dala miliyan 53 sun maƙale.

A ranar 23 ga Janairu, 2020 kotu ta yanke hukuncin cewa dole Emefiele ya bayyana “a yi masa shari’a kan rantsuwar da ya shafi hanyoyin da kake da su ko kuma ka samu, tun daga ranar da aka ba da cikakken umarni, na biyan bashin Dala miliyan 53 a halin yanzu kuma za a biya a ƙarƙashin wannan umarnin kuma ya nuna dalilin da ya sa ba za a tura shi kurkuku ba na rashin biyan kuɗin.”