Daga BASHIR ISAH
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya faɗa ranar Talata cewa, akwai masu fakewa da addini domin cimma manufofinsu a ɓangaren tattalin arziki da siyasa.
Buhari ya ce akwai buƙatar ci gaba da bai wa fannin ilimi muhimmanci domin tafiya da galibin jama’a.
Shugaban ya yi waɗannan kalaman ne a birnin Nouakchott, Mauritania, yayin da suke ganawa da Rashad Hussain, Jakadan Amurka kan ‘yancin harkokin addini.
Yayin tattaunawar tasu, Buhari ya tuno ganawarsa da tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump a fadar White House inda ya ce Trump ɗin ya tambaye shi kan cewa: “Me ya sa kake kashe Kiristoci a Nijeriya.”
Inda Buharin ya ce masa matsalar ba ta addini ba ce, ta manyan laifuka ce, inda wasu ke fakewa da addini don neman ƙarfafa tattalin arziki da kuma siyasarsu.
A cewarsa, “Matsala ce wadda Nijeriya ta daɗe tana fama da ita, wanda hakan ba daidai ba ne.
“Wasu mutane sun fake da addini, amma ta hanyar ilimantarwa yanzu jama’a sun gane.
“Mutane da dama na so su yi addini ba tare da wata matsala ba, yayin da wasu kuma suka fake da matsalolin addini don cimma manufofinsu.
“Idan aka ilimantar da jama’a suna iya gane masu amfani da addini don biyan buƙatunsu. Galibi, suna yin haka ne don abin duniya.
“Haka nan, idan wasu suka ga sun gaza sai su rika ba da uzurori iri-iri, ciki har da lamarin addini,” in ji Buhari.
A nasa ɓangaren, Ambasada Hussain na Ƙasar Amurka ya ce, Amurka na da sha’awar haɗa kai da Nijeriya a fannin ilimi don samar da lumana a fannin addinin ƙasar.
“Akwai abubuwa da yawa da za mu iya yi tare domin wanzar da zaman lafiya da zaman tare mai armashi.
“Muna sha’awar abin da kake yi, kuma za mu yi farin cikin ganin mun agaza a inda ya dace,” in ji Jakadan.