Bologna na tattaunawa da ɗan bayan Jamus Mats Hummels, mai shekara 35, wanda ba shi da ƙungiya bayan da ya bar Borussia Dortmund, yayin da ƙungiyar ta Italiya ke neman wanda zai maye gurbin Riccardo Calafiori mai shekara 22, wanda ke shirin tafiya Arsenal.
Getafe za ta samu sama da fam miliyan 5 ne kawai daga cinikin sayar da Mason Greenwood fam miliyan 26.7 daga Manchester United zuwa Marseille, saboda yaerjejeniyar da suka yi lokacin da suka karɓi aron ɗan wasan na Ingila mai shekara 22 daga Old Trafford a bara.
Ɗan gaban Scotland Oli McBurnie, mai shekara 28, na shirin tafiya Las Palmas ta Sifaniya a matsayin wanda ba shi da ƙungiyar bayan da Sheffield United ta rabu da shi a bazaran nan.
Kyaftin ɗin Rangers James Taɓernier, mai shekara 32, na tattaunawa da ƙungiyar Turkiyya, Trabzonspor wadda a shirye take ta biya fam miliyan 1 a kan ɗan wasan ɗan Ingila.
Haka kuma ƙungiyar ta Scotland a shirye take ta saurari tayi a kan Todd Cantwell, inda ƙungiyoyi da yawa na Ingila ke son sa.
Chelsea ta bayyana sha’awarta ta sayen mai tsaron ragar Ɓillarreal Filip Jorgensen ɗan Sweden mai shekara 22.
Ƙungiyar gasar Championship, Derby County na shirin sayen mai tsaron ragar Sweden Jacob Widell Zetterstrom, mai shekara 26, inda ƙungiyar ta cimma farashin fam miliyan 1.4 da ƙungiyarsa Djurgardens IF.
Arsenal na son ɗan wasan gaba na gefe na Athletic Bilbao Nico Williams, mai shekara 22, da ɗan wasan tsakiya na Real Sociedad Mikel Merino, mai shekara 28, amma kuma tana fuskantar gogayya daga Barcelona a kan ’yan wasan tawagar Sifaniyan biyu.
Borussia Dortmund da Juɓentus, da kuma Paris St-Germain, kowacce na son sayen Jadon Sancho amma kuma babu ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ta iya biyan kuɗin da Manchester United ta sa masa, fam miliyan 40.
Manchester City na tattaunawa domin sayar wa Borussia Dortmund ɗan bayanta na Brazil Yan Couto, wanda har yanzu bai fara taka mata leda ba, inda take sa ran ƙungiyar ta Jamus ta biya fam miliyan 25 kan ɗan wasan mai shekara 22.
Ita kuwa Manchester United ta taya Matthijs de Ligt yuro miliyan 40 (fam miliyan 33.6) amma kuma Bayern Munich ta ce ba za ta karɓi abin da ya gaza yuro miliyan 50 (fam miliyan 42.2) ba a kan ɗan wasan na Hollland tare da ƙarin wasu kuɗaɗen a kan ɗan wasan mai shekara 24.
Ana ganin ɗan bayan Chelsea Treɓoh Chalobah ya kaɗu bayan da ƙungiyar ta ƙi tafiya da shi wasanninta na shirin tunkarar sabuwar kaka a Amurka, kuma ɗan wasan mai shekara 25 na ganin ana son a yi watsi da shi ne daga ƙungiyar.
Ƙungiyoyin Saudiyya biyu na sha’awar ɗan bayan Ingila Kieran Trippier, mai shekara 33, duk da cewa saura shekara ɗaya a kwantiraginsa da Newcastle United, wadda daman yana shirin barinta.
To amma shi kuwa ɗan wasan tsakiya Joelinton, na Brazil mai shekara 27, ya ce yana jin daɗin zamansa a Newcastle United kuma ya yi amanna, Bruno Guimaraes takwaransa na Barzil mai shekara 26, zai ci gaba da zama a ƙungiyar shi ma duk da rahotannin da ake yi cewa zai tafi.
