Hajji: NAHCON ta cire amfani da Dala

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da cire amfani da kuɗin Dala wajen biyan kuɗaɗen da suka shafi aikin Hajji, matakin da ya ke da nufin rage tashin gwauron zaɓin kuɗin aikin Hajji.

Shugaban Hukumar Na ƙasa, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ne ya sanar da hakan a yayin ziyarar ban girma da ya kai wa Sarkin Argungu a fadarsa.

Shugaban ya bayyana cewa, biyan muhimman kuɗaɗen ayyukan Hajji, kamar jiragen sama da dala ya taimaka matuƙa wajen tsadar farashin Hajji, wanda hakan ya sa ’yan Nijeriya da dama ba su iya biya.

Saleh ya yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa tallafin da ta ke bayarwa musamman tallafin aikin Hajji, sai dai ya nuna damuwarsa kan yadda ake jinkirin biyan kudin aikin Hajji, lamarin da ya sa Nijeriya ta gaza cike kason da aka ware mata na maniyyata.

Ya yi kira ga shugabannin gargajiya da na addini da su taimaka wajen sauƙaƙa kawar da dala a harkokin da suka shafi aikin hajji ta hanyar shigar da masu ruwa da tsaki.

Saleh ya ƙara da cewa, yayin da maniyyata ke biyan Umrah a Naira, kamfanonin jiragen sama da sauran masu ba da sabis na dagewa kan biyan dala don aikin Hajji, wanda hakan ke haifar da cikas ga ɗimbin maniyyata.

Shugaban ya jaddada cewa magance wannan matsala na iya haifar da raguwar farashin aikin Hajjin 2025.

By ukarofi