Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Nijeriya da haɗin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Gijira ta Nijeriya sun karɓi ’yan Nijeriya guda 310 da da aka koro su daga Jamhuriyar Nijar ranar Litinin.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka yaɗa a shafin Tiwita ranar Laraba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa reshen jihar Kano, ta halarci bikin karɓar ‘yan gudun hijira ɗari uku da goma (310) tare da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta ƙasa da ƙasa da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta ƙasa.
“Waɗanda suka dawo sun isa makarantar horar da shige da fice da ke Kano da ƙarfe 2210, inda NEMA da sauran masu ruwa da tsaki suka tarɓe su.
“Mutane 310 da suka dawo an kasasu kamar haka: manya mata: 98, manya maza: 41, yara maza: 85, yara mata: 86.”
