Hajjin 2023: Nijeriya ta yi rashin alhazai 13 a Saudiyya – NAHCON

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya, NAHCON, ta bayyana cewa, aƙalla mutum 13 daga cikin mahajjatan Nijeriya 95,000 da suka halarci Hajjin bana ne suka riga mu gidan gaskiya yayin Hajjin 2023 a Saudiyya.

NAHCON ta ce da fari mutum bakwai sun rasu kafin Arfa sannan shida a Arfa.

Da yake jawabi a wajen taron bayan kammala Arfa da aka shirya ranar Lahadi a Makka, shugaban tawagar likitocin NAHCON, Dr. Usman Galadima, ya ce mahajjata huɗu suka kwanta dama a Arfa, biyu a Mina, wanda hakan ya sa jimillar alhazan Nijeriya da suka rasu yayin aikin Hajjin ya kama mutum 13.

Dr. Galadima ya ƙara da cewa, an samu mata biyu da suka haihu, sai kuma mutum uku da suka kamu da ƙurarrajin ƙarambau.

Haka nan, ya ce “daga cikin ƙalubalan da aka fuskanta a Mina har da matsalar rashin tsafta da yawan cunkoson jama’a.”

A cewar Dr. Galadima, adadin marasa lafiya 25,722 da aka duba su yayin aikin Hajjin, 15,268 mata ne sannan 10,454 maza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *