Daga MAHDI MISA MUHAMMAD
Gwamnatin Jihar Ebonyi a ƙarƙashin Gwamna Francis Ogbonna Nwifuru ta amince da fitar da sama da Naira amiliyan 500 don tallafa wa maniyyata arba’in da shida masu zuwa aikin hajjin 2025.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Ebonyi Jude Chikadibia Okpor ne ya bayyana hakan.
A cewarsa, an amince da hakan ne a yayin taron majalisar zartarwa ta jihar Ebonyi a ranar Juma’a 7 ga watan Fabrairu, 2025 wanda ya gudana tare da shugaban majalisar kuma gwamnan jihar Ebonyi, Francis Ogbonna Nwifuru.
Ya ce; “Nijeriya ƙasa ce da ba ruwanmu da addini, kuma Ebonyi a ƙarƙashin jagorancin gwamna mai ci, ta zama gidan zaman lafiya ga kowa da kowa inda ake ƙarfafa haƙuri da addini.
“A cikin baje kolin manufar wannan gwamnati, an amince da fitar da jimillar miliyan ɗari biyar da hamsin da ɗaya, Naira dubu ɗari biyar da biyu, kobo tamanin da huɗu (N551,502,142.84) domin ɗaukar nauyin ayyukan hajjin mutum arba’in da shida. Kowane mutum ɗaya zai samu N8,784,085.59 a cikin wannan kuɗi.
An kuma ƙuduri aniyar neman dukkan shugabannin majalisar da su yi la’akari da ɗaukar nauyin mutum ɗaya (1) a kowace aaramar hukuma a aikin Hajjin 2025 don faɗaɗa halartar ‘yan asalin ƙasar.”
An bayar da rahoton cewa, a ranar 20 ga watan Janairu, Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Shugaban Zartaswa, Farfesa Abdullahi Usman ya sanar da farashin jigilar mahajjatan 2025 a Saudiyya.
Farfesa Usman ya ce sanarwar kuɗin ya biyo bayan amincewar ofishin mataimakin shugaban ƙasa da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki domin a samu sauƙi.
A cewarsa, maniyyata daga jihohin Kudu za su biya N8,784,085.59, yayin da waɗanda suka fito daga shiyyar Arewa kuma za su biya N8,457,685.59.
Alhazai daga Borno da Adamawa za su biya mafi ƙarancin N8,327,125.59. Farfesa Usman ya alaƙanta hakan ne da samun haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki da suka haɗa da wakilai daga fadar shugaban ƙasa da ƙungiyar manyan sakatarorin gudanarwa na hukumar jin daɗin alhazai ta jihohi.
Farfesa Usman ya ce “An cimma wannan ƙoƙarin kan kuɗin ne bayan tuntuɓa mai yawa don tabbatar da haɗewa cikin wannan muhimmin tsari na yanke shawara,” inji Farfesa Usman.
Ya kuma yaba da irin goyon bayan da fadar shugaban ƙasa ke bayarwa, musamman Ameen Amshi, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan ayyuka na musamman, da ƙungiyar manyan sakatarorin gudanarwa na hukumar jin daɗin alhazai ta jiha, da hukumomi, da kwamitoci.
Shugaban NAHCON ya buƙaci maniyyatan da ke da niyyar bin ƙa’idojin Saudiyya tare da jaddada muhimmancin biyan kuɗi da wuri da kuma yin rajista a kan lokaci domin gujewa ƙalubale.