MRS ya rage farashin man fetur zuwa N925 a lita

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yanzu haka dai Kamfanin MRS yana sayar da man fetur akan Naira 925 a kowace lita a dukkan gidajen mansa ta da ke faɗin Legas.

Wannan rage farashin ya faru ne kwanaki bayan da kamfanin matatar Dangote, abokin aikin MRS, ya rage farashin sari zuwa Naira 890 kan kowace lita.

Haka zalika, kamfanin ya sanar da cewa, za a sayar da farashin man fetur a kan Naira 935 a kan kowace lita a yankin Kudu maso Yamma, N945 a Arewa da kuma N955 a Gabas.

Kamfanin ya sanar a ranar Litinin a shafinsa na ɗ (tsohon Tiwita) cewa yanzu haka MRS na sayarwa a kan sabon farashin yankin.

“Farashin na iya bambanta, amma abu ɗaya ya tsaya iri ɗaya – muna ba ku ingantaccen mai wanda ke sa injin ku ya yi aiki mai kyau,” inji MRS. 

“Idan kun ga wani gidan man MRS da ake sayarwa sama da wannan farashi, muna buƙatar ku kira ko ku tura mana saƙo ta imel.”

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur zuwa N890 a ranar 1 ga Fabrairu.

Matatar mai ta Dangote ta rage farashin man fetur daga N950 zuwa N890, daga ranar Asabar 1 ga Fabrairu, 2025.

Wannan gyare-gyaren farashin yana mayar da martani ne ga ci gaba mai kyau a fannin makamashi na duniya da kuma raguwar farashin ɗanyen mai a duniya.

Wata sanarwa daga matatar man Dangote, wanda babban jami’in kula da harkokin kasuwanci na ƙungiyar Anthony Chiejina ya fitar, ta bayyana cewa, wannan sabon mataki ya biyo bayan wani mataki makamancin haka da aka yanke a ranar 19 ga watan Janairu, lokacin da aka aiwatar da karin farashin ɗanyen mai kaɗan saboda tashin farashin danyen mai.

Sai dai kuma, da yanayin kasuwannin duniya na baya-bayan nan da ke nuna koma baya, matatar man Dangote ta sake daidaita tsarin farashinta, inda ta samar da sauƙi ga ‘yan Nijeriya.

Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, rage farashin man fetur zai yi matukar rage farashin man fetur a faɗin ƙasar, tare da samar da sakamako mai kyau a duk faɗin tattalin arzikin ƙasar.