Falana ya maka kamfanin Meta a kotu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Lauyan kare haƙƙin ɗan Adam kuma Babban Lauyan Nijeriya, Femi Falana, ya shigar da ƙara inda ya nemi niyyar dalar Amurka miliyan 5,000 a gaban wata babbar kotu a Legas kan kamfanin Meta mai Facebook mallakar Mark Zuckerberg da ke Amurka, bisa zargin kutsawa cikin sirrinsa.

A cikin gabatar da ƙudirin bisa ga sashe na 37 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da sashe na 24 (1) (A) da (E) da Sashe na 34 (1) (D) na Dokar Kare Bayanai ta Nijeriya 2023, doka ta 2 tsari na 1 na haƙƙin ɗan adam, 2009, Lauyan Babalomi, ya zargi cewa Meta na yaɗa hotuna da murya mai taken, “AfriCare Health Centre,” a shafinsa na yanar gizo, inda ya nuna cewa Falana ya kamu da wata cuta da aka fi sani da ‘Prostatitis’, wadda lauyan ya yi ikirarin cewa duk ƙarya ne kuma ya saɓa wa sashe na 37 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya, 1999.

Falana ya yi ikirarin wallafa bidiyon ta dandalin www.facebook.com, “ƙarya ne, kuskure, yaudara da rashin adalci wanda ya saɓa wa tanadin sashe na 24 (1) (a) da (e) na Dokar Kare bayanan Nijeriya 2023.”

Bayan haka, yana nemi kotu ta ba da umarni ga waɗanda ake ƙara nan da nan su cire, share su goge bidiyon da aka yi wa taken “Cibiyar Lafiya ta AfriCare akan dandalinsu,  www.facebook.com.”

Dangane da diyyar, Falana, ya nemi a biya shi diyyar dala miliyan 5, 000 (dalar Amurka miliyan biyar) da kuma umarnin kotu da ta ga ya dace ta bayar a cikin lamarin.

Falana wanda ya yi ikirarin cewa faifan bidiyon karya da aka wallafa game da yanayin lafiyarsa, wato rayuwarsa ta sirri ta ɓata masa suna da kuma sunan da ya gina tsawon shekaru.

Ya ƙara da cewa, wallafar da wanda ake ƙarar ya yi na ƙarya, mai ban haushi da kuma tada hankali yana sanya shi a cikin wani yanayi na rashin jin daɗi, wanda hakan ya haifar masa da ruɗani.