Sojojin sama sun sake kuskuren halaka fararen hula a Katsina

Daga BELLO A. BABAJI

Kimanin fararen hula
shida ne sun rasu a yayin da wani jirgi mai tashin angulu na sojojin sama ke gudanar da wani atisaye akan ƴan ta’adda a Jihar Katsina.

Rhotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Zakka dake ƙaramar hukumar Safana a ranar Asabar, a lokacin da sojojin suka sako wasu ababen fashewa daga sama, kamar yadda wasu mazauna yankin suka shaida wa manema labarai.

Sojojin sun kai harin ne bayan da ƴan bindiga suka farmaki sansanin ƴan sanda da kashe jami’ai biyu da wani ɗan banga.

Wani mazaunin ƙauyen ya ce sojojin sun kawo ɗauki ne a lokacin da ƴan bindigar suka janye, inda a nan ne aka rasa mutane shidan, waɗanda bakiɗayan su ƴan gida ɗaya ne.

Sada, wanda ɗaya ne daga cikin shaidun ya ce an karɓo gawawwakinsu ne a buhuna, waɗanda aka yi jana’izarsu kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Saidai, ƙungiyar kare haƙƙin ɗan-adam ta ‘Amnesty International’ ta ce mutane 10 ne suka rasa rayukansu, kamar yadda ta faɗa a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, inda ta buƙaci a gaggauta gudanar da sahihin bincike game da lamarin.

Kawo yanzu dai rundunar sojoji ba ta ce komai ba game da batun.

A watan Junairu, an samu wani harin sojoji da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 16 a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara a lokacin da suka farmaki ƴan bindiga.

Haka ma a watan Disambar 2024 a Sakkwato, inda aka rasa mutane 10 da jikkata wasu shida a ƙauyuka biyu, a lokacin da sojoji suka farmaki mayaƙan Lakurawa.

Hallau, a Disambar 2023 ne wani harin sojoji ta sama ya yi sanadiyyar hallaka mutane 85 a wajen taron maulidi a lokacin da sojoji suka farmaki ƴan ta’adda a yankin Tudun Biri a Jihar Kaduna.