Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumomin Saudiyya sun sanar da cewa za su fassara huɗubar ranar Arafat ta aikin Hajjin shekarar 2026 zuwa harsuna 35 na duniya ciki har da Hausa da Yarbanci domin musulmi a sassan duniya su amfana da saƙon huɗubar.
Shugaban kula da harkokin addini na Masallacin Harami da Masallacin Annabi, Sheikh Abdulrahman bin Abdulaziz Al-Sudais ne ya bayyana hakan yayin da mahajjata ke ci gaba da isa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.
Ya ce huɗubar ranar Arafat da Sheikh Ali bin Abdulrahman Al-Hudhaifi, limami kuma mai wa’azi a Masallacin Annabi da ke Madina zai gabatar, za a fassara ta zuwa harsuna 35 tare da yaɗa ta ta hanyoyin sadarwa na zamani da kafafen yada labarai masu alaka da hukumar kula da harkokin addini.
Al-Sudais ya bayyana cewa matakin na daga cikin kokarin da masarautar Saudiyya ke yi wajen isar da saƙon Musulunci ga musulmi a faɗin duniya tare da bai wa waɗanda ba Larabawa ba damar fahimtar huɗubar ranar Arafat.
Ya ƙara da cewa hukumar ta samu gogewa sosai a aikin fassara hudubar cikin shekaru da suka gabata, inda ya ce manufar shirin ita ce kara haɓaka ilimin addini cikin harsuna daban-daban.
Daga cikin harsunan da za a yi amfani da su wajen fassara hudubar akwai Turanci, Faransanci, Indonesiya, Urdu, Turkanci, Farisanci, Sifaniyanci, Sinanci, Rashanci, Bengali, Hindi, Malay, Amharic, Hausa, Swahili da Yarbanci.
