Hajojin Afirka na matuƙar jawo hankalin jama’ar ƙasar Sin

Spread the love

Daga CMG HAUSA

An buɗe bikin sayayyar hajojin Afirka ta yanar gizo karo na hudu a jiya, inda aka sayar da kayayyakin Afirka ga jama’ar ƙasar Sin ta yanar gizo.

Manazarta suna ganin cewa, bisa yanayin tinkarar cutar COVID-19, bikin ya sa ƙaimi ga yin sayayya a cikin kasar Sin, kana zai taimakawa raya haɗin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka.

Tun daga shekarar 2019, an riga an yi irin wannan biki har sau uku, wanda ya jawo kamfanoni da masu kashe kuɗi da dama, waɗanda suka halarci bikin, kuma hakan ya sa ƙaimi ga yin sayayya.

Bisa ƙididdigar da hukumar kula da harkokin cinikayya ta ƙasar Sin ta yi, yawan kuɗin da aka samu a ƙasar Sin ta hanyar yin sayayya ta yanar gizo, a gun bikin na tsawon kwanaki 15 na shekarar 2021, ya kai kuɗin Sin Yuan biliyan 700.

An ce, a wannan karo za a gwada barasa, da kofi, da ruwan ’ya’yan itatuwa da sauransu daga ƙasashen Afirka ta Kudu, da Tanzania, da Ruwanda, da Benin da sauransu, a yayin bikin da aka shirya kai tsaye ta yanar gizo.

Bisa ƙididdigar da aka yi, an ce, a cikin shekara daya da ta gabata, yawan cinikin da aka gudanar tsakanin Sin da Afirka ya ƙaru bisa yanayin tinkarar cutar COVID-19, kana yawansa ya karu da kashi 35.3 cikin ɗari, wanda ya kai matsayin koli a tarihi.

A cikin wannan adadi, yawan kayayyakin da aka shigar da su daga Afirka zuwa ƙasar Sin, ya karu da kashi 40 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.

Mai Fassara: Zainab

By Editor