Ofishin Jakadancin Sin a Saliyo ya bai wa Musulmi kyautar kayan abinci

Daga CMG HAUSA

Ofishin jakadancin Sin dake ƙasar Saliyo ya miƙa kyautar kayayyakin abinci ga al’ummar musulmi, albarkacin watan azumin Ramadan, da kuma bikin cikar ƙasar shekaru 61 da samun ’yancin kai, wanda ya fado ranar Laraba.

Yayin mika kayan tallafin a jiya Alhamis a birnin Freetown, fadar mulkin ƙasar, jakadan Sin a Saliyo Hu Zhangliang ya ce, kayayyakin sun ƙunshi shinkafa, da man girki, da fulawa, da sikari.

Ya ƙara da cewa, “Ina miƙa saƙon murna ga shugaba Julius Maada Bio, da gwamnatin Saliyo, da ɗaukacin al’ummar ƙasar, don gane da ƙoƙarinsu wajen bunƙasa fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban daban.” Ya kuma jinjinawa gwamnatin ƙasar game da kyautatawa rayuwar mabiya addinin Musulunci da ke ƙasar.

Hu ya ƙara da cewa, ko shakka babu al’ummar musulmin Saliyo ta yi rawar gani, wajen yauƙaƙa kyakkyawar alaƙar dake tsakanin Sin da Saliyo, don haka yake fatan ta hannun waɗanda aka damkawa kayayyakin, tallafin zai isa ga mabuƙata cikin al’ummar ƙasar.

Da yake bayyana godiya a madadin gwamnatin Saliyo, ministan ma’aikatar walwala da jin dadin jama’a Bendu Dassama, ya jinjinawa ofishin jakadancin na Sin. Yana mai cewa tallafin ya zo a daidai gabar da ake buƙatarsa, kamar yadda ƙasar Sin ta saba yi a ko da yaushe.

Mai Fassara: Saminu