Hamas ta sako fursunonin Isra’ila uku a musayar Palastinawa 183

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Asabar ne mayaƙan Hamas ta sako ƙarin wasu fursunonin Isra’ila guda uku akan musayar Palastinawa 183 da Isra’ila ta sako a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

An gudanar da wakoki gabannin musayar a birnin Deir Al-Balah a safiyar Asabar da jami’an bada agaji na Red Cross da wasu ƴan Hamas suka jagoranta.

Jami’an Red Cross ne suka gabatar da fursunoni ukun ga sojojin Isra’ila a yankin Kudancin ƙasar inda suke karɓar kulawar lafiya a matakin farko.

Wata sanarwa da hukumomin tsaro na Isra’ila suka fitar, ta ce sun yi kira ga al’umma da su kiyaye fitar da bayanan waɗanda aka sako da na iyalansu ba tare da amincewasu ba, da kuma neman a riƙa kula da irin haka yayin sako wani sahun fursunonin.

A yayin da aka bayyana hotunan ƴan Isra’ilan da aka sako a yanayi na galabaita, Firaministan ƙasar, Benjamin Netanyahu, wanda ya je ziyara a Amurka, ya aiko da saƙo ga hukumomin da su tabbatar da an warware matsalolin karya wasu dokoki da Hamas take yi a yayin kammala harkokin tsagaita wutar.