Hanyoyin amfani da man jojoba 

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

A matsayin man fuska:

A shafa ɗan kaɗan bayan an wanke fuska yayin da take da ɗan ɗumi (damp).

Cire kayan kwalliya:

A zuba shi a kan auduga (cotton pad), a goge fuska domin cire makeup da datti mai ɗauke da mai.

ƙara ƙarfi ga nan shafawa:

A haɗa ɗan kaɗan da man shafawa jiki ko cream domin ƙarin lafiya ga fata.

Haka kuma ana iya amfani da shi a wuraren da suka bushe, ko wuraren da ke da tauri a jiki, ko wajen rage kaikayi bayan aski, ko magance eczema.

Masana sun janyo hankali kan lamarin man jojoba inda suka ce a nemi na asali, ma’ana kada a yi amfani da wanda aka sarrafa a kamfanonin kayan shafe-shafe wanda hakan zai tabbatar da yana ɗauke da cikakken sinadaran gina fata tare da tsallake yiwar haɗuwa da wani abu da aka saka da zai iya zama illa. 

Haka kuma sun ƙara da cewa, ko da yake man jojoba yana da wuya ya haifar da matsala, ana ba da shawarar a yi gwajin ɗan kaɗan (patch test) kafin amfani gaba ɗaya, domin tabbatar da cewa babu wata rashin jituwa tsakaninsa da fata.

Jojoba oil ya zama ɗaya daga cikin manyan sinadaran kula da fata a duniya saboda yadda yake haɗa ilimin kimiyya da sauƙin amfani. Daga shayar da fata ruwa zuwa yaƙi da tsufa da kuma warkar da matsalolin fata, wannan man ya tabbatar da kansa a matsayin mafita mai inganci ga duk wani mai son kula da lafiyar fatarsa cikin salo na zamani ko na ƙwararru.

By ukarofi