Hanyoyin magance matsalar bushewar leɓe

Daga AISHA ASAS

Masu karatu barkanmu da sake saduwa a shafin kwalliya na jaridar al’umma, Blueprint Manhaja. A yau dai za mu kawo wasu daga cikin hanyoyin da za a bi don kare leɓe daga matsalolin da muka ambata a makon da ya gabata. Idan kun shirya, mu tsunduma cikin darasin: 

Leɓe na ɗaya daga cikin gaɓoɓin jiki da ke bayyane ba tare da kariya ta tufa ko makamancin su ba, don haka, haƙƙi ne da ya rataya akan mammalinsa samar masa kariya ta hanyar kulawa. Akwai hanyoyi da dama da za ki iya kula tare da kuvutar da leɓenki, don haka za mu kawo wasu daga cikinsu.

Dole ne amfani da man baki ga wadda ke son ganin leɓenta cikin walwala, sai dai yana da matuƙar muhimmanci kisan irin man da na ki leven ke buƙata da kuma yanayin da ake ciki, ma’ana zafi ko sanyi.

A dinga sanya shi akai akai don ganin ba a bar leɓen a bushe ba. A yanayi na zafi leve na buƙatar a shafa masa mai sau uku zuwa huɗu a rana. Yayin da lokacin sanyi yake buƙatar fiye da hakan. A lokacin sanyi kana buƙatar man baki duk bayan ‘yan awanni ko mintoci, ya danganta da yanayin wurin da kake.

A lokacin da ake iska na hunturu, leɓenki na buƙatar kariya daga gare ki kamar yadda kike rufe hannu da ƙafafunki don kare su daga cutarwar sanyi, shima leɓen zai yi kyau idan an rufe shi ta hanyar saka takunkumi ko makamantan sa.

Haka ma lokutan zafi, a lokacin da rana ta tsananta, leɓenki na buƙatar suturcewa don kare shi daga cutarwar da zafin rana ka iya yi masa.
Shan ruwa masu yawa hanya ce babba da ke kare leɓen daga cutukan da ka iya kawo tasgaro ga walwalar sa. Da yawa muna ganin kamar shan ruwa na taimakon mu ne kawai don kawar da ƙishirwa, sai dai ko kaxan ba haka ba ne, ruwa na taka muhimmiyar rawa a jikin ɗan Adam, wanda rashin su babbar illa ce ga ayyukan da jikin ɗan Adam ke yi, ciki kuwa har da leve.

Rashin isassun ruwa a jiki na kai leɓe ga bushewa, sava da kuma tsagewa, don haka yake da matuƙar muhimmanci yawaita shan ruwa a cikin kowanne irin yanayi, ma’ana sanyi ko zafi.

Nisanta kai da lasan leɓe, domin yana da illa fiye da amfani. Za ka iya ganin abin kamar yana taimakon leɓen, sai dai a lokacin da yawun baki ya jiƙa leɓe, na ɗan lokacin da zai yi a jiƙen ne kawai za ka ji dadi, sai dai da zaran ya bushe, albarkacin yawun sai fatar leɓen ta bushe fiye da yadda ake tsammani. Wannan ba abin mamaki ba ne, duba da cewa ko a jiki yawu suka zuba, matuƙar sun samu bushewa a wurin, idan ka taɓa, za ka ji wurin ya bambanta da sauran. 

Ki guji ɓare saɓar leɓe, domin hakan na ji wa fatar ciwo, wanda zai iya kawo wata matsalar daban, kamar fitar jini, jin zafi yayin da wani abu ya taɓa wurin ko kuma wasu daga cikin cutukan da fatar da ta ɗaye ke fuskanta a lokacin da ta ci karo da ƙwayoyin cuta.

Daga ƙarshe, a dinga sauraren ƙorafin leɓe, a kula a sanya ido sosai kan matsalar sa da kuma warkewar ta, domin matsalar leɓe na saurin tafiya idan an ba ta abin da take buƙata, don haka jinkirin tafiyar na buƙatar gaggauta ganin likita, domin akwai cutukan da ke amfanin da matsalolin don sanar da mamallakin gangar jikin ga su sun iso, ciki kuwa har da kansa.