Shin mijinki ya cancanci girmamawa? (1)

Daga AISHA ASAS

Annabin rahma (SAW) ya ce, “da zan umarci wani ya yi wa wani sujjada, da na umarci mata ta yi wa mijinta sujjada.”

Sujjada ita ce ƙololuwa idan aka yi zancen darajanta wani abu, itace ke nuni da ƙasƙantar da kai ga wanda aka yi wa tare da tabbatarwa ya fi ka ta kowanne ɓangare. 

Annabin rahma ya yi amfani da ita ne don nuna daraja da ƙimar miji a wurin matarsa, duk da cewa ya san ba zai yiwu hakan ta kasance ba, domin ba wanda ya cancanci sujjada sai wanda ya halicci mai aikata ta. Sai dai da wannan kwatancen ne ƙwaƙwalwa za ta samu damar zana tsayin darajar miji. Shi ya sa aka yi amfani da kalmar ‘da’, ma’ana da zai yiwu hakan ta kasance, sai dai ba za ta kasance ɗin ba. Abin nufi dai hikimar zance ne aka yi amfani da shi.

Idan mai karatu ya gama ayyana nisan darajar miji, za mu ci gaba ne kan matsayin da miji yake da a al’adance. Tunda muna ɓangaren hausawa, za mu fara da kallon darajar da Bahaushe ya ba wa miji.

Kamar yadda muka sani, bahaushe ya ɗauko al’adarsa ne ya cakuɗe da addini, ma’ana, a lokacin da addinin Musulunci ya zo wa bahaushe, ya karɓe shi, sai ya ɗauko al’adarsa ya gwama da shi, don ganin bai yi rashin wasu daga cikin al’adun ya saba da su. Wannan ce ta sa, za ka samu wasu daga cikin ababen da bahaushe ke iƙirarin addini ne, al’adar sa ce ya gwama da wani hukunci na addini, ya masa kwaskwarima don ya tafi daidai da ra’ayin shi.

A vangaren aure ma hakan ce ta kasance. Shehu Usmanu Ɗanfodiyo Allah ya qara masa rahma ya ce, “sukan ɗauki mata kamar tukanen dafa abinci. Su yi amfani da su don dafa abinci, su ci kawai.” (Kafin zuwan Musulunci). Idan zan yi tafsirin maganar tasa, zan ce, sukan azabtar da mata, tamkar yadda tukunya ke shan azabar wuta yayin da take ƙoƙarin mayar da ɗanye dafafe.

Kuma sukan yi ta kansu ne kawai idan suna buƙatar biyan buƙatar sha’awarsu. Kamar dai yadda aka sani, ana bi ta kan tukunya ne kawai idan ana buƙatar ta dafa abinci, domin ba mu tava ganin an yi adon ɗaki ko an kai wa baƙin kunya abinci da tukunya ba.

Wannan ɗabi’a ta bahaushe akan matarsa da Mujaddadi ya faɗa, yana magana ne na kafin zuwan Musulunci gare su. Sai dai idan muka yi duba da yanzu da Musulunci ya gama biye jikinmu, ya tasiri ko rashin tasirin wannan furuci yake? 

Musulunci ya ce, “matayenku gonakinku, ku zo wa matanku a lokacin da kuke so.”

Sai ya yi kwaskwarima ya mayar da shi ba dalilin da zai sa mace ta kauce wa buƙatar mijinta, ko tana ciwo, ko tana jin yunwar da ya bar ta da ita, ko ya mata duka har ya ji mata rauni. Kai wasu na ganin ko jinin al’ada take yi idan yana da muradin hakan bai da matsala.

Musulunci ya qara cewa, “idan matanku suka yi maku laifi, ku masu nasiha, idan sun qi ji, ku ƙaurace wa shimfiɗar su, idan sun ƙi ji, ku kai ƙararsu ga magabatansu, idan sun ƙi ku dake su.”

A cikin duk waɗannan dukan ne kawai ya yi daidai da shi malam bahaushe, don haka sai ya tunkuɗe duk sharuɗɗan uku na farko, ya dira kan na ƙarshe don daidaita shi da kansa. Ta hanyar amfani da addini wurin ganin ya mayar da matarsa jaka. Har wa yau, bahaushe ne ya danne sanin yadda Musuluncin ya ce ayi dukan ya ɗauko nasa dukan ya mayar addini.

Idan muka dawo kan sha’ani na fita ga matar aure, bahaushe ya yi ƙoƙarin amfani da ƙarfin ikonsa wurin ganin ya zaunar da matarsa a gida irin zaman da yake so, don haka ba shi da mafita face ɗauko ra’ayi ya cakuɗe da addini, a wannan ƙoƙarin na sa har ya shiga hurumin addinin, wato ya haramta abin da Allah ya halasta. Misali; irin kuble da ake yi a gidajen wasu ɓangarori na Hausawa. Sun mayar da shi addini, amma idan anbi tsarin na su, aka kalli abin da idon basira, za a tarar ba komai ciki face son kai, ba komai na addini da yake ciki. Misali, ka kuble matarka, ba ta zuwa ko ziyara, ko iyayenta sai ta yi daqar kake barin ta ta je, ina ka samo hakan a addini.

Ka haramta mata zuwa Masallaci, alhali addini ya halasta hakan idan tana da sha’awa. Ka ɗauko wasu al’adu da suka hana ɗan uwanta na jini shigowa gidanka ya ganta, kai kuma ka hana ta zuwa kai masa ziyara don sada zumunta. Duk ina ka samo waɗannan a cikin addini.

Idan har muka tsunduma cikin mu’amalar mijin Bahaushe da matarsa, za mu fahimci har yau matarsa baiwa ce a wurinsa, abin amfani a zubar a lokacin da aka gama cin moriyar ta. Duk da cewa ba a taru aka zama ɗaya ba, da yawa na kula tare da daraja matansu kamar yadda Musulunci ya koyar.

Rashin ba wa mata darajar da Allah ya ba su da kuma irin gallazawar da suke fuskanta a gidan miji na ɗaya daga cikin dalilan da ka iya sa su kasa ganin girman mazajensu. Sai dai abin tambaya a nan, shin don mijinki bai ba ki darajar da Allah ya ba ki ba, shi zai sa ki kasa ba shi darajar da girman da Allah ya ba shi?