Zaɓen APC: Sanata Adamu ya ƙaddamar da kwamitocin gudanarwa

Daga BASHIR ISAH

A ranar Lahadin da ta gabata Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ƙaddamar da kwamitocin da za su ja ragamar gudanar da zaɓen fidda gwani na takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar.

Taron ƙaddamarwar ya gudana ne a Sakatariyar APC da ke Wuse 2, Abuja.

APC za ta gudanar da zaɓen nata ne daga ranar 6 zuwa 8 ga Yuni, 2022, a dandalin Eagle Square da ke Abuja inda za ta tasayar da ɗan takararta na Shugaban Ƙasa a 2023.