Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Gwamnatin Tarayya ta ayyana cewar, za ta farfaɗo da matacciyar ƙasa kimanin murabba’in kilomita 22,000, ta kuma inganta rayuwar ‘yan Nijeriya kimanin miliyan 20 nan da shekarar 2030.
Ministan lura da muhalli, Alhaji Mohammed Abdullahi shi ne ya yi furucin haka a makon nan yayin gudanar da wata bitar ƙara wa juna sani kan ƙarfafa kuzarin gudanar da ayyuka da kuma fayyace tsarin manufar shirin nan na yin kadarko ko garkuwa daga kwararowar hamada (GGW) da aka gudanar a birnin tarayya na Abuja.
Shirin, wanda aka tsara domin tafiya bai ɗaya da duniya kan bunƙasa manufar koren launi na ECO-DRR da hukumar ƙasa kan yin kadarko wa koren launi, tare da haɗin kan shirin Majalisar Ɗinkin Duniya kan yanayi ta tsara.
Ministan, ya samu wakilcin darakta kan dabaru, bincike da ƙididdiga na ma’aikatar sa, Mista Stanley Jonah ne a wajen bitar.
Abdullahi ya bayyana cewar, shirin zai bayar da matuƙar muhimmanci ne wa jihohi guda 11 da matsalar kwararowar hamada ta yi wa katutu, yana mai ƙara cewar waɗannan jihohi sun mallaki kashi 35 na ɗaukacin murabba’in ƙasa da Nijeriya take zaune akai.
“Hukuma ta NAGGW tuni ta ƙaddamar da yin nazari akan kwatankwacin ƙasar noma da waɗannan jihohi 11 suka mallaka, nusar da al’ummomin su, faɗakar da su, shuka bishiyoyi da sarrafa ƙasa da Allah ya huwace masu, inganta yanayin rayuwa, samar da kayayyakin aiki, haɗi da samar da ayyuka wa jama’a.
“Shirin da a yanzu yake kan gudana ya ƙunshi farfaɗo da dawo da albarkatun ƙasa domin inganta rayuwar jama’a, haɗi da sukunin sarrafa ƙasa yadda zai dace da canjin yanayi.
“Harwa yau, shirin ya jivanci darajanta ƙasa domin yin ayyukan gona da zummar ƙara wadatar aminci ta hanyar jurar canjin yanayi da samar da kayayyakin masarufi da za su bunƙasa tattalin arzikin jama’ar karkara,” inji shi.
Minista ya kuma bayyana cewar, Gwamnatin Tarayya tana ɗaukar dukkan matakan da suka dace wajen sassauta hatsarukan dake akan canjin yanayi, ƙarancin abinci, illolin ƙona daji da iska mai gurɓata yanayi bisa amfani da ‘yan kuɗaɗen dake akwai.
Ya ce shirin ana gudanar da shi ne da zummar farfaɗo da kula da ƙasar noma a sahin hamada domin kawar da gurɓacewar ƙasa dake haddasa talauci a tsakanin al’umma.
Darakta-Janar na hukumar, Dokta Yusuf Maina-Bukar ya bayyana cewar, hukumar su ta dawo da martabar ƙasa yayin da ta girka ko gina katangar bishiyoyi da ta kasance gandagarki wa hamada mai tsawon kilomita 389.46.
Maina-Bukar, ya samu wakilcin mai riƙon darakta ta hukuma wacce tsarin shirye-shiryen gudanarwa ya rataya a ofishinta, Mrs. Habiba Ibrahim.
“Hukumar ta ƙudura niyyar gina kadarko mai tsawon kilomita 13, 000 da kuma dasa itatuwan kariya daga hamada mai murabba’in hekta 250, 000 da murabba’in hekta 250, 000 a wuraren da wannan shiri ya shafa.
“Wannan shiri yana da zummar inganta ayyukan gona domin ƙarfafa rayuwar jama’a daga nan zuwa shekara ta 2030.
Shi ma wani babban jami’i mai lura da tabbatuwar wadatar abinci ta hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya, Dokta Oluseyi Fabiyi ya faɗi cewar, hukumar ta taimaka matuƙa gaya wajen faɗaɗa shirin na GGW a nahiyar Afirka.
“Waɗansu ƙalubalolin da suka jiɓanci farfaɗo da martabar ƙasa shi ne waɗansu yankunan da shiyyoyin suna ɗauke da duwatsu da yashi.”
