Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Cibiyar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma (CITAD), ta horar da ‘yan jarida masu binciken ƙwaƙwaf dabarun ɗauko labaran cin hanci da rashawa da yaɗa shi, ga ‘yan jaridu 20 da suka fito daga arewacin Nijeriya.
Horarwar da ta gudana a cikin kwana 2, an yi ta ne a Pali Suite da ke Unguwar GRA ta jihar Bauchi.
A jawabinsa, shugaban CITAD Yunusa Zakari Ya’u ya ce, maƙasudin shirya bitar shi ne sun lura cewa yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya ba ya samun nasarar da ya kamata ya samu.
Ya ƙara da cewa: “‘Yan jarida na da rawar takawa wajen wayar da kan jama’a, domin ba za ka yaƙi cin hanci da rashawa ba sai ka nusar da al’umma sun gane illar sa.”
Ya cigaba da cewa, “su kansu al’umma na ƙasa-ƙasa su rinƙa bada ta su gudunmawar ta hanyar ƙyamatar wannan ɗabi’a, su ƙaurace wa mutanen da suke facaka da kuɗin al’umma, su tabbatar cewa duk mutumin da aka naɗa muƙamin Kansila ko Ciyaman to su bincike shi su tabbatar cewa bai yi sama da faɗi da kuɗin su ba.”
Ɗaya daga cikin waɗanda su ka yi maƙala a wurin Dr. Jamila Muhd. Ɗahiru wace kuma Malama ce a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya a tsangayar aikin jarida ta ce akwai buƙatar ɗan jarida ya siffantu da wasu halaye matuƙar yana so ya bada gudunmawa wajen ɗauko rahoton cin hanci da rashawa, inda ta ce: “Na farko shi kansa ya kamata ya guji cin hanci da rashawa, ta ce idan kana son ka yaƙi abu dole sai ka ƙi shi, na biyu shi ne ya kamata ya zama ya kamata a ce yana da ilimin abin domin rashin iliminsa zai iya sa ya aikata wannan abin ba tare da sani ba.”
Ta ƙara da cewa, “na uku ya kamata ya zama ya na tsakiya kar ya goyi bayan wancan vangaren ko wannan ɓangaren, na huɗu shi ya kasance ya na da ƙwaƙƙwarar hujja domin shi kansa rashin hujja mai ƙarfi cin hanci da rashawa ne,” ta bakin Dr. Jamila.
Taron bitar dai ya samu halartar malaman jami’a kamar: Farfesa Habu Muhd. Fagge, Auwal Musa Rafsanjani Shugaban CISLAC Abuja, gogaggun ‘yan jarida masu binciken ƙwaƙwaf da sauran masu ruwa da tsaki a fannoni daban-daban.
