Har yanzu ba a sabunta wa kamfanin Airtel lasisin zamansa a Nijeriya ba – NCC

Spread the love

Daga UMAR M. GOMBE

Hukumar Kula Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta ce har yanzu ba ta amince da sabunta wa kamfanin sadarwa na Airtel lasisin gudanar da harkokinsa ba a Nijeriya saɓanin iƙirarin da shugaban kamfanin a Nijeriya, Mr. Olusegun Ogunsanya, ya yi.

Daraktan Sahen Hulɗa da Jama’a na NCC, Dr. Ikechukwu Adinde, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Lahadin da ta gabata.

NCC ta tabbatar da cewa lallai kamfanin Airtel ya aika da takardar neman sabunta lasisin zamansa a Nijeriya, amma hukumar ba ta amince da hakan ba tukuna.

NCC ta ci gaba da cewa an ja hankalinta kan wani rahoto da aka wallafa a intanet inda aka ruwaito Mr. Olusegun Ogunsanya ya ce an sabunta wa kamfanin Airtel lasisin zamansa a Nijeriya na wa’adin shekaru 10 masu zuwa.

An ruwaito Mr. Ogunsanya ya faɗi haka ne a wajen wani taro da kamfanin Airtel ya gudanar a ranar 14 ga Yulin 2021 a jihar Legas.

Lamarin da NCC ta ce ba haka yake ba saboda a cewarta, takardar neman sabunta lasisin da kamfanin Airtel ya miƙa mata tana kan bin matakan da suka dace kafin amincewa da ita.

By Editor