Har yanzu kamfanin NNPC ne kaɗai ke sayen fetur daga matatar Ɗangote

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Har yanzu Kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPCL, ne kaɗai ke riƙe da ragamar sayen man fetur daga matatar mai na Dangote duk da umurnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar a baya-bayan nan na sakar wa sauran ’yan kasuwar mara wajen sayen mai kai tsaye daga matatar.

‘Yan kasuwar man fetur sun bayyana a ranar Larabar da ta gabata cewa, NNPC zai ci gaba da zama shi kaɗai ke sayen mai daga matatar ta Lekki har sai an ƙulla wata sabuwar yarjejeniya da matatar mai ta Dangote.

Sai dai ba su bayyana lokacin da yarjejeniyar tsakanin ƙungiyoyin biyu za ta ƙare ba. Su ma jami’an NNPC da matatar mai na Dangote ba su mayar da martani kan lokacin da yarjejeniyar za ta ƙare ba.

A ranar 11 ga Oktoba, 2024, gwamnatin tarayya a cikin wata sanarwa daga ma’aikatar kuɗi, ta sanar da cewa a yanzu ‘yan kasuwar man sun samu ‘yancin sayen man fetur daga matatar Dangote ba tare da NNPC ya shiga tsakani ba.

“Ta ci gaba da cewa, masu sayar da albarkatun man fetur yanzu suna iya sayen mai kai tsaye daga matatun mai na cikin gida ba tare da aikin tsaka-tsakin na NNPC ba. Ana ƙarfafa masu kasuwa da su fara sayayya kai tsaye daga matatun mai akan sharuɗɗan kasuwanci da aka tattauna tsakanin juna, wanda zai haɓaka gasa tare da inganta kasuwar man,” inji sanarwar.

Amma bayan ganawa da jami’an matatar man Dangote a ranar Talata, mambobin ƙungiyar ‘yan kasuwar man fetur mai zaman kanta ta Nijeriya sun bayyana cewa har yanzu kamfanin na NNPC shi ne kaɗai mai karɓar man Dangote har sai an kammala yarjejeniya tsakanin Dangote da NNPC.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta aika wa ‘yan kungiyarungiyar ta IPMAN a shiyyar Yamma, wanda Shugaban shiyyar Kudu maso Yamma, Dele Tajudeen, ya fitar, ƙungiyar ta ce, “Mataimakin shugaban ƙungiyar IPMAN ta ƙasa, shugaban shiyyar Yamma, ’yan IPMAN, da Shugaban PTD na shiyyar sun gana da su. Mataimakin Shugaban Rukunin Dangote da wasu fitattun ma’aikatan matatar man Dangote a ranad, 15 ga Oktoba, 2024.

By ukarofi