Sarkin Machina ya yaba da salon jagorancin Shettima na ƙarfafa hukumar NEDC

Spread the love

Daga GAMBO ISA

Mai Machina, Alhaji Dr. Bashir Albashir Bukar OON, LONN, kuma Sarkin Machina na 77 a jihar Yobe ya yaba da nasarorin da shiyyar Arewa maso Gabas ta samu tun lokacin da aka ƙirƙiro Yobe daga tsohuwar jihar Borno a 1991 zuwa yau.

Mai Machina ya bayyana hakan yayin zantawarsa da jaridun Blueprint a Abuja.

Sarkin ya yaba da ci gaban da aka samu a fannin shirye-shiryen noma, gina hanyoyin sadarwa da ke kawo shawarwarin jagoranci ga jama’ar yankin Arewa maso Gabas.

Mai Machina ya kuma yaba wa, mai girma Gwamna Mai Mala Buni (Chiroman Gujba) da irin salon jagorancin gwamnatinsa bisa jajircewarsa na bunƙasa noma, ƙarfafawa ƙananan hukumomi da sauransu, inda ya yi alƙawarin bada goyon baya ga gwamnati.

Mai Machina, ya buƙaci ‘yan ƙasar da ke yankinsa da su yi amfani da kyakkyawan shugabanci kamar yadda mai girma gwamna Mai Mala Buni ya yi kira da su bai wa shugaban ƙaramar hukumar irin wannan goyon baya.

Ya kuma buƙaci talakawansa da su ci gajiyar shirin bunƙasa noma na gwamnati.

Mai Machina, ya yi kira ga matasa a masarautunsa da jiha da su zama jakadun ƙasa nagari, su guji shaye-shayen ƙwayoyi, su saurari shawarwarin iyayensu.

Kazalika ya buƙaci masu hannu da shuni da masu hali a cikin al’umma da su tallafa wa matasa a shirye-shiryen koyon sana’o’i domin dogaro da kai don zama shugabanni na gaba.

Sarkin ya jajentawa gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Borno da Shehun Borno kan bala’in ambaliyar ruwa da ta afku a ƙaramar hukumar Maiduguri da Jere a kwanakin baya, ya kuma yi kira ga ƙungiyoyi da su tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta raba da gidajensu kwanan nan.

Mai Machina ya yaba wa hukumar (NEDC) ta ci gaban Arewa maso Gabas bisa ayyukan ci gaban al’umma daban-daban a jihohin arewa maso gabas sannan ya yaba da salon jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima bisa kula da ayyukan hukumar.

By ukarofi