Kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, ya bayyana cewa matatar mai ta Fatakwal (PHRC) ba ta fara sayar da mai ba ko buɗe shafin saye tukuna, domin har yanzu ana kammala muhimman ayyuka.
Jami’in hulɗa da jama’a na NNPCL, Olufemi Soneye, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a. Ya ce a halin yanzu, kayayyakin da ake siyarwa daga PHRC suna zuwa ne daga kamfanin tace mai na Ɗangote, tare da ƙarin kuɗaɗe da kukumar kula da harkokin man fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta ƙayyade. Kayayyakin PHRC suna samuwa kawai ga gidajen sayar da mai na NNPCL a wannan mataki, inda ake daidaita farashi lokaci-lokaci dangane da yanayin kasuwanci.
Kamfanin ya gargaɗi jama’a da su yi watsi da duk wata jita-jita game da sauyin farashin kayayyaki, yana mai cewa za a sanar da jama’a a hukumance idan har aka yi wani gyaran farashi. Wannan ya biyo bayan kiran jama’a na fara aiki da cikakken iko a matatar man Fatakwal, yayin da ake ci gaba da daidaita tsarin aiki.
A gefe guda, NNPCL ta ƙaryata rahoton da ƙungiyar PETROAN ta bayar cewa PHRC tana aiki da kaso 70 na ƙarfin ta. Kamfanin ya tabbatar da cewa a halin yanzu an fara tace mai a tsohuwar tashar da ke da ƙarfin ganga 60,000 a kowace rana, yayin da sabuwar tashar tace man da ke da ƙarfin ganga 200,000 tana nan a gyare kuma za ta fara aiki nan ba da jimawa ba. Dukkanin tashoshin suna cikin wurin da ake kira Alesa Eleme a Jihar Ribas.