Mai sayar da maganin bindiga ya harbi kanshi a ciki

Daga USMAN KAROFI

Wani mai maganin gargajiya mai suna Ismail Usman ya ji raunukan harbin bindiga yayin da yake gwada sahihancin maganin bindiga a unguwar Kuchibiyi da ke ƙaramar hukumar Bwari, a babban birnin tarayya.

Wani mazaunin unguwar, Samson Ayuba, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis lokacin da mai maganin ya harbi kansa a ciki don gwada ingancin maganin da ya ƙera. Ya ce mai maganin ya faɗi nan take, kuma maƙwabta suka garzaya da shi asibiti domin ceton rayuwarsa.

Kakakin rundunar ’yan sandan FCT, SP Adeh Josephine, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce mai maganin ya yi amfani da bindigar da ya ƙera don harbin kansa a ciki, amma maganin ya kasa kare shi. Jami’an ’yan sanda daga sashen Byazhin sun kai masa agaji kuma suka garzaya da shi zuwa asibitin Kubwa kafin daga bisani aka mayar da shi asibitin Koyarwa na jami’ar Abuja a Gwagwalada don ƙarin kula.

Ta ƙara da cewa bincike ya nuna cewa an samu bindigar gida da kuma magunguna iri daban-daban a gidan mai maganin. Rundunar ta ce za a gurfanar da shi gaban kuliya kan mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba da kuma yunƙurin kashe kansa, kamar yadda Sashe na 231 na dokar laifuka ya tanada. Kwamishinan ’yan sandan FCT, Olatunji Rilwan Disu, ya yi tir da lamarin, yana mai jan hankalin jama’a kan haɗarin mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba da kuma irin wannan halin na jefa kai cikin hatsari.