‘
Daga BELLO A. BABAJI
Jami’an rundunar ƴan sandan Nijeriya sun yi nasarar kama wasu mutum biyar akan iyaka, waɗanda ake zargin su da laifin safarar haramtattun makamai.
Kakakin rundunar, ASP Muyiwa Adejobi ya faɗi hakan cikin wata takarda da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce waɗanda aka kama dukkaninsu maza ne da suka haɗa da; Adamu Noma, Matthew Audu, Andrew Poyi, Aminu Sani da Aminu Talha.
Ya ce jami’an Tawagar Leƙen Asiri ta FIDIRT ne suka kama su a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2024.
Adejobi ya ce bayan kama su ne aka kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK47 na gida guda 10 da bugun Isra’ila guda biyar, sai ƙaramar bindiga (pistol) da alburusai 20 da kuma na’urar sarrafa makamai.
Ya ƙara da cewa, Sufetan ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya bai wa jami’an umarnin ɗaiɗaita duk wani haramtaccen makami da aka kama da inda ake sarrafa shi.
Ya kuma ce za su cigaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen ayyukan fashi da ta’addanci a dukkanin sassan Nijeriya.