Har yanzu ‘yan Nijeriya na fama da matsalar tsaro lokacin Tinibu – Dauda

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Ƙasa da watanni biyu da soma mulkin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinibu al’umma na cigaba da bayyana damuwarsu kan kamun ludayin gwamnatin musamman a ɓangaren tsaro.

A cewar galibin waɗanda Jaridar Manhaja ta zanta da su sun bayyana damuwar su, kan yadda duk da alƙawurran da gwamnatin Tinibun ta yi wa ‘yan ƙasa kan lamarin tsaro, al’umma ke cigaba da ɗanɗana kuɗar su sakamakon har-haren ‘yan bindiga musamman ma a jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Kwamared Bishir Dauda Sabon Unguwa Katsina, shi ne Babban Magatakardan Ƙungiyar Muryar Talaka a Nijeriya, a zantawar da wakilinmu a Sakkwato Aminu Amanawa, ya ce har yanzu talakawa na fama da matsalar tsaro musamman ma dai a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.
Gadai yadda tattaunawarsu ta kasance:

Ka fara da gabatar wa masu karatu da kanka?

Suna na Kwamared Bishir Dauda Sabon Unguwa Katsina, ni ne Babban Magatakardar Ƙungiyar Muryar Talakan Nijeriya.

Ku ne za a ce wakilan talakawan nan, takamaimai wane hali Arewa take ciki, ko kuma ya kuke ganin halin da Arewa ta sami kanta?

To gaskiya zan iya cewa muna cikin yanayi mai hatsari, musamman batutuwan da suka jiɓanci rashin tsaro, zaka ga cewa kila wannan Gwamnati ta Bola Ahmed Tinubu, an samu ƙarin kai hare-hare a Arewacin Nijeriya, an yi rikici na ƙabilanci da abin yi a jihar Filato kusan jihar Benuwai, yana da wahala a yi sati baka ji an kashe mutane ba, ba abinda ya faru, in ka zo jihar Katsina har yanzu ana ɗauke mutane, ana kashe mutane. 

Sannan in ka zo jihohin Sakkwato da Jihar Zamfara da Kebbi Kaduna da Neja mutane suna cikin uƙuba, an hana mutane su yi noma dole sai sun biya kuɗin fansa, sannan za a ba su dama su yi amfani da gonakinsu. Ba zan mance ba, farko-farkon hawan wannan gwamnati an je Tangaza aka kashe mutane, an je irin su Maradun A jihar Zamfara da Maru da wasu ɓangarori na jihar Zamfara, an kashe manoma.

Amma ita wannan matsalar ta tsaro Kwamared matsala ce da za a iya ɗora wa gwamnati, tun da ana ganin matsalar ta fara ne wa gwamnatocin da suka gabata?

Eh to, ita gwamnati dama ɗorawa ne, kuma a gwamnati idan wata ta hau za ta gaji abinda ake ce ma “asset”, duk wasu abubuwa na cigaba gwamnati za ta gajesu, sannan kuma za ta gaji matsalolin gwamnati, saboda haka alhakin gwamnatin da ke ci ne, ta magance waɗannan matsalolin. Duk gwamnatin da ta zo ta fara cewa ita wannan matsalolin ba ita ta haddasa su ba, to wannan gwamnati ba ta san abinda ta ke yi ba, ba ta san ciwon kanta ba. 

Kuma wannan ɗorawa gwamnatin baya laifi shi ne ya sa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kasa cimma nasara, na kawar da matsalar tsaro, saboda haka a cikin alƙawurran da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ‘yan Nijeriya ya ce zai kawar da matsalar tsaro, ni na karanta wannan kundin da ya buga.

To amma ba za a ce kila kun yi gajin haƙuri ba, ganin cewa ita tafiyar nan yanzu aka fara?

A’a, Amanawa!

Mutane wannan idan ba a kashe mi shi ‘yan uwa ba wannan an sace shi ko an sace mishi ɗan uwa zai ce an yi gajin-haƙuri kenan?

Amma da yanzu haka maganar nan da mu ke yi yanzu haka suna hannun  ‘yan daji, suna cikin daji wa su ma an kashe su na lahira, to shine za ka ce an yi gajin-haƙuri? Ai Murtala Muhammad tsohon shugaban Nijeriya, na mulkin soja wanda ya yi mulkin soja a 1975 ai cikin watanni shida ya yi abubuwan da aka gani, duk da za a ce mulkin soja ne amma ana iya gane inda shugaba ya dosa a cikin ‘yan kwanakin saboda wannan ‘yan kwanakin da ka ke gani, kwana talatin wata rana sai ka ji an ce an yi shekara huɗu cif ta zo.

 To shi ya sa mu ke ganin ba za mu yi kwanciya ba mu ce lokaci yanzu-yanzu ne aka fara a zo a yi mana sakiyar da ba ruwa! Yanzu ka ga hanyar nan da ta taso daga Funtuwa zuwa Sakkwato kullum sai an kashe mutane sai an tare mutane, kuma babbar matsalar da ake fama da ita babu dare ba rana babu maraice babu safiya ko wane lokaci ana iya tare motoci sun je kasuwa a sace su a yi cikin daji da su.

Haka kenan a iya cewa ku a matsayin ku na Ƙungiyar Muryar Talaka, ba ku yi na’am da shi ba?

A matsayinmu na Muryar Talaka muna ganin Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gaza warwas zuwa yanzu! Don haka burinmu su tsaya idan aiki suka zo.

Amma kana maganar ta gaza warwas! Ana ganin ga shirye-shirye nan tana fitowa da su, Alal misali matsalar tsaron nan da fara da sauke manyan Hafsoshin tsaro wannan ba wani ƙoƙari ba ne da ta ke na samar da tsaro ga ƙasa?

Kusan ko wacce gwamnati tun daga Obasanjo lokacin da ya hau a 1999 ya yi wa sojojin ritaya ma su yawa, ciki har da manyan sojoji, lokacin da aka zo aka kawo su Yusuf  Burutai suma suka zo suka fara, ba su yi komai ba aka cire su, wannan Faruku Yahaya wannan ɗan Kaduna ɗin nan shi ma ba abinda su ka yi, matsalar ba ta kawar ba, sannan yanzu an zo kan Lagbaja da sauransu.

Ka ga cire jami’an tsaro kawai ka canja su, ka koma ka yi kwanciyarka cikin “Villa”, ba zai kawo ƙarshen matsalar tsaro ba. Saboda haka mutane su daina kuskuren ɗaukar cewa canja jami’an tsaro wai shi ne wani mataki, ba mataki ba ne ba.

Amma ba ka ganin Hausawa sun ce “Idan kiɗa ya canza, rawa ma dole ta sauya” tun da an canza jami’an tsaron nan wataƙil salon yaƙin ya sauya?

To, ai bai sauya ba, abinda ake yi na a zo a ɗora duwatsuna kan hanya ana amshe kuɗaɗe wurin direbobi shi ne ake yi har yanzu, ai bai canza ba. Abinda mu ke tunanin canzawar shine a shiga daji don har abada in dai akwai daji akwai duwatsu har abada Nijeriya ba za ta zauna lafiya ba.

Amma don ka zo bakin kwalta ka yi aza shinge ai ba zai magance wannan matsalar tsaro ba. Saboda haka ni har abada idan ba a je maɓoyarsu ba aka je aka magance matsalar ba, maganar gaskiya zan ce za a magance matsalar bai taso ba. Saboda haka ka ga kenan kiɗi ya canza, amma rawar ba ta canza ba. Tun da dai ‘yan ta’addan nan ana barinsu suna ci gaba da hawa baburansu suna zuwa garuruwa suna kashe mutane da ci gaba da garkuwa da jama’a.

Me ku ke so ita wannan gwamnati ta Bola Tinubu ta yi da zai sa a ce kun yi na’am da kamun ludayinta?

Na farko dai, in dai da gaske wannan gwamnati ta ke yi, ba kawai maganganun iska da aka saba ji ga sauran shuwagabannin da suka wuce shi ne dole a tura jami’an tsaro cikin da ji, su je su fatattaki mutanen a maɓoyarsu. Zancen su zauna sai an kawowa mutane hari sannan su rugo su ce za su taimaki mutane, ban cin an kashe mutane an sace na sacewa ba zai yiwu ba! Dole ne a tura waɗannan sojojin.

Kuma  wanda shi ne shugaban askarawan sojojin Nijeriya shi ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Saboda haka shi ke da wannan haƙƙi na ya bai wa wannan Hafsa shin dama su je su shiga cikin dajin nan, su fatattake su. Abu na gaba, dole gwamnonin na Arewa su san da cewa sai sun bawa wannan matsalar tsaron muhimmanci. Yawwa kuma dole ne su had’a kansu.

Ya zamana cewa suna meeting kuma suna ɗaukar mataki na idan ba a yi meeting ba a cimma matsaya kuma ba za a wofintar da ita ba. Kuma zancen wani gwamna ya zo ya ce zai yi sasanci da ‘yan ta’adda ko ma su aikata laifi, mu talakawan Nijeriya ba mu aminta da wannan ba

Saboda me ya sa ba za ku amince ba tunda ana neman  hanyar da za a magance wannan matsalar ba?

Tun da aka ƙirƙiri duniya ake sata, ake kisan kai, ake aikata laifuka ka tava ganin an daina? To ta ya zaka ce zaka sasanta da wannan mai aikata wannan abin sannan a ce a daina? Ai ba a haka! Ta’addanci ba a sasanci kan shi, don sata ba a daina ta. Idan har za ka yi ta sasantawa da ɓarayi to tabbas sabbi za a dinga samu. Don haka ƙarya ce duk wanda zai zo ya yaudari mutane.

Don haka ku Muryar Talaka ba kwa goyon bayan duk wani shiri da ya shafi sulhu?

Ka tava ganin an yi sulhu da ɓarawo? Ɓarayin waya ka tava ganin ana sulhu da su? Ɓarayin babura ka tava ganin ana sulhu da su? Ba a sulhu da ‘yan ta’adda! Ka gane, ba a sulhu da su. Yaƙarsu ake yi. Yawwa, shi ne amfanin gwamnati.

To amma ta ya za a yaƙi wanda wataqil ba gaba da gaba ya ke fitowa yana aiwatar da ayyukan shi ba?

Har masallacin Juma’a suna zuwa, ko kwanan nan da suka tava tare hanya nan tsakanin Gusau da Tsafe a wani gari har sallar Juma’a suka yi. Ai ba aljanu ba ne ba, an san su. Ga wurare nan da yawa na gaya maka tun daga Funtuwa har Sakkwato duk inda ka ga ana yawan tare mutane ka je dajin wurin ko duwatsuna an san inda su ke.

Ba fa yaƙarsu za a yi ba Amanawa, yawwa shi ya sa mu ke maganar cewa indak dagaske yak’arsu za’ayi to dole ne a shiga a yak’esu fata fata. Mutum idan ya zo ya tuba shima dole ne a hukunta shi, saboda shiyasa mu ke da dokoki.

Amma ba shi yuwa mutum yana kisan kai, ya na ta’addanci yana satar mutane yana amsar kuɗin fansa sannan kuma ka zo ka ce za ka sasanta da shi ka yafe mai, to shiyasa ba za a sami maslaha ba. Dan haka mu Bama goyon bayan gwamnan da zai zo ya ce zai yi sasanci da su.

Kuma dole ne waɗannan gwamnonin na Arewa su cire bambamcin siyasa da waɗanda suke NNPP na jihar Kano da waɗanda su ke PDP kamar Zamfara da APC dole ne ya zamana su mai da hankali a kan wannan matsalar tsaron, saboda gaskiya maganar gaskiya abinda ya sa ka ga ina ta magana a kan matsalar tsaron nan, saboda matsalar tsaron nan tana hana ilimi tsakanin ‘ya’yanmu.

Tana hana noma, yanzu ba ma maganar noman zamani ake ba, domin kuwa karya ce kawai har zuwa yau ba a zamanantar da noman zamani ba. Yanzu maganar da ake su je ma su yi noman abin ya gagara. Mutanen da aka kai wa hari a Ƙaramar Hukumar Tangaza, ai kuɗin da za su biya ‘yan ta’adda ne ba su ba da ba aka je aka kai mu su wannan harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *