Wata mai koyon sana’a ta sace yaron uwargijiyarta a Neja

Daga BASHIR ISAH

Bayanai daga Jihar Neja sun wata mai koyon sana’ar gyaran suma ta sace yaron matar da take koyon sana’ar a wajenta a shagonta da ke babbar kasuwar Minna, babban birnin jihar.

Majiyarmu ta ce yaron dablamarin ya shafa, Chinedu Chukwueke, watansa shida da haihuwa.

Mahaifin yaron, Chikezie Stanley Chuks, shi ne ya bayyana mummunan labarin a shafinsa na Facebook.

Inda ya ce, “Barka da rana, an ɗauke mini yarona ɗan wata shida da haihuwa mai suna Chinedu Chukwueke a shagon matata yau Lahadi, 23 ga Yuli, 2023 a kasuwa Kure, Minna.

“Idan aka samu muhimman bayanai game da yaron a kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa, ko kuma a tuntuɓi lambar waya, 07033186837.”

Kazalika, mahaifin yaron ya wallafa makamancin wannan saƙon a shafinsa na Twitter.

Ya ce matar “Ta zo ta fake ne da koyon aiki a shagon matata sai ta sace yaron. Ga ma lambar wayarta, 09032876441,” in ji baban yaron.

Ƙoƙarin da majiyarmu ta yi don jin ta bakin iyayen yaron kai tsaye ya ci tura. Kuma ya zuwa haɗa wannan labari, ‘yan sandan yankin ba su ce komai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *