Sheikh Dakta Yusuf Ali (Sarkin Malaman Gaya)

An haife shi a cikin garin Gaya ta Jihar Kano a shekarar 1950. Ya haddace Alƙur’ani ya na da shekara 11, ya gama duk wani fanni na ilimi da ake karantawa a makarantun soro (ƙarshen ilimi kenan a wancan lokacin) yana da shekaru 15.

Ya fara rubutun Alkur’ani yana da shekaru 13, ya zama Alaramma mai darasu tun ina da shekaru 14.Tsangayar sa tana nan a halin yanzu a Gashua, a Katuzu/Garin Yamma, jihar Yobe.

Malam Musa Dan Dikkware shi ne Halifa sa mai darasu a halin yanzu. Ya fara shimfiɗa buzu na karantar da ɗalibai a makarantar soro tun daga Gashua Katuzu, har zuwa Kano a gida mai lamba 32 Chiranci, tun yana Shekaru 14.

Malaman sa sun haɗa da Mahaifana da Mallam Ali Ɗan Gunka, da Sheikh Muhammadu Arabi, duk a Gaya. A Jihar Borno da Yobe, na zauna a duk wata Tsangaya da ta yi suna da tashe a wancan lokaci; kamar Girgir, Jakusko, Alagarno, Jaba, Badigana, Bindigi, Jajere, Nangere, Kolere, Koriyal, Abbari da sauransu. Saboda haka ban san iyakar malamaina ba, sai dai kamar Mallam Haruna Mai Dogon Gemu, da Sheikh Muhammadu Jinjiri, a Gashua, amma a Kano Sheikh Uthman Qalansawy ne.

Har yanzu fa ban shiga Sakandare ba, kuma ban yi aure ba, don ko balaga ban yi ba, haka na ci gaba da karantar da Alkur’ani da ilimai, da buɗewa da gudanar da makarantun Islamiyya, da rubuta Alƙura’anai har 1971.

Daga 1971, nan na buɗe wani sabon shafi na rayuwa ta ilimi, inda na shiga makarantar sakandire ta School For Arabic Studies, SAS da ke Kano. Na gama a shekarar 1974. Na yi Diploma a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, Na yi digiri na ɗaya, da na biyu da na uku a jami’ar Bayero da ke Kano, sai na zama Dakta. Na kuma samu kyautar girmamawa na dakta daga jami’ar Albart, ƙasar Canada.

Na yi bautar ƙasa a shekarar 1982. Bayan haka kuma na halarci kwasa-kwasai da dama da tarurruka na ƙara wa juna ilimi, ciki da wajen Nijeriya.

Aiki kuwa na fara a shekarar 1974, a inda na fara da Court Scribe har zuwa Chief Clerk; kuma daga Assistant Registra har zuwa Higher Registrar; kuma daga Area Court Judge har zuwa Upper Sharia Court Judge; daga nan na zama Ddarakta na Sharia a kotun ɗaukaka ƙara ta Shari’a, sai na bar aiki a shekarar 2009.

Na riqe muƙaman siyasa da yawa. Na ziyarci wasu ƙasashe na Turai da Afrika da ƙasashen Larabawa. Na yi aikin Hajji sau 31, na yi Umra fiye da 200. Na kuma fara bayyana a media (kafofin yada labarai) a shekarar 1971, kawo yau.

Ni ne farkon wanda fara amsa tambayoyin Addinin Musulunci ta Telephone (live) a kafafen yaɗa labarai, sannan kuma ni ne na fara amsa dukkan tanbayoyin da suka shafi Addini da rayuwa ta duniya da lahira, a sani na dai ban ji wani ba har yanzu! Alhamdu lillah.

Ni ne farkon wanda ya fara bincike da warkar da Cututtuka da Alƙur’ani domin tun ina da shekaru 14 na fara a Gashua. Na rubuta waƙoƙi sun fi 1000 (dubu), da mas’aloli da yawa a harshen Hausa da Larabci.

Ina zaune a unguwar Tudun Maliki, Kano Nijeriya. Mata na Uku, ’ya’ya na 36, babbar su Bilkisu, ƙaramar su Husna, mai wata 19.

Ba abin da na fi so kamar ninƙaya cikin ruwa (swimming) da rubuta waƙa (poetry), da bincike Alhamdu Lillahi.

An yi wannan Rubutun tun 14 Nov 2013.
Yusuf Ali Yusuf

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *