Babu gudu ba ja da baya game da janye ‘yan sanda masu gadin shafaffu da mai – Runduna

Daga BASHIR ISAH

Rundunar ‘Yan Sanda ta Nijeriya ta ce babu abin da zai sa ta janye matakin da ta ɗauka na janye jami’anta daga bai wa masu ƙumbar susa (VIPs) a ƙasar.

Wannan na zuwa ne bayan mako guda da rundunar ta ƙaryata janye jami’an kwantar da tarzoma daga bai wa shafaffu da man kariya cikin wata takardar sirri da ta fito fili.

Bayan ce-ce-ku-ce kan ƙaryata batun da rundunar ta yi, wasu ‘yan ƙasa na ra’ayin ‘yan sandan ba su da niyar aiwatar da tsarin.

Sai dai, da yake maida martani kan batun cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi, ya ce rundunar na nan kan bakanta game da matakin janye jami’an nata.

Ya ce, “Rundunar na sanar da cewa matakin janye jami’an PMF daga rakiya da gadi ya tabbata daram. Babu ja da baya game da wannan muhimmin sauyin.”

Ya ce an fara aiwatar da sauyin ne ta hanyar fara aiki da rahoton kwamitin da aka kafa kan batun ya miƙa.

Ya ƙara da cewa, ɗaukar wannan mataki ɓangare ne na ƙoƙarin da rundunar ke yi wajen taƙaita kashe kuɗaɗe da kuma inganta ayyukan rundunar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *